Posts

Showing posts from February, 2017

YA KAI MAI NEMAN KUSANCI

Idan kaga mutane sun nuna wadatuwarsu da duniya, kai kuma sai ka wadatu da Allah. Idan kuma kaga suna nuna farin cikinsu da duniya, To kai kuma kayi farin ciki da Allah. Idan kaga mutane suna debe kewarsu da duniya, kai kuma ka sanya debe kewarka (wato samun nutsuwarka) da Allah. Idan kaga mutane suna neman shiga wajen Sarakunansu da manyansu, suna neman kusanci dasu domin su samu Girma da daukaka, to kai kuma ka nemi kusanci da Allah da kuma Soyayyarsa ta wannan hanyar zaka samu Mutukar girma da daukaka. NASIHA CE DAGA ZAUREN FIQHU (07064213990) - (31-01-2017).