Posts

Showing posts with the label sallama

HUKUNCIN AMSA SALLAMAR WANDA BA MUSULMI BA

TAMBAYA TA 2001 ******************** Assalamu alaikum. Allah ya qarawa malam Eamani ya jiqan iyaye. Ameen, tambaya nake roqon a amsa min. Yaya hukuncin Wanda ya shaaku da Wanda ba musulmi ba kuma ya dauke shi a matsayin aboki? kuma shin ya kamata a mayar ma Wanda ba musulmi sallama  idan yace ma Assalamu alaikum?. Dafatan malam zai samu damar amsa tambayata. daga dalibinka Ibraheem I g AMSA ******* Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Allah Madaukakin Sarki ya umurcemu da cewa kada mu riki Yahudu da Nasaara amatsayin Masoya ko Majibinta garemu. Ba don komai ba, sai domin sharrin da irin hakan zai haifar ga rayuwarmu da addininmu. Allah Madaukakin Sarki yace : "YA KU WADANDA SUKAYI IMANI! KADA KU RIKI YAHUDU DA NASAARA AMATSAYIN MAJIBINTA (WATO ABOKAI KO MASOYA) SASHENSU MAJIBINTA NE GA SASHE. DUK WANDA YA JIBINCESU DAGA CIKINKU TO HAKIKA SHIMA YANA CIKINSU. HAKIKA ALLAH BA YA SHIRIYAR DA MUTANE AZZALUMAI". (Ma'idah ayah ta 51). Ibnu Abi Hatam ya ...