Posts

Showing posts with the label hamzah

QISSAR YAQIN BADAR KASHI NA TARA

AN FARA GWABZAWA TSAKANIN JARUMAI Acikin kashi na takwas mun tsaya ne adaidai wajen da Kowanne bangare sukayi sahu sahu, kuma Manzon Allah (saww) yayi addu'a yana cewa: "Ya Allah Ga Quraishawa nan sun tunkaro da Alfaharinsu, suna jayayya da kai, kuma suna Qaryata Manzonka.. Ya Allah taimakon nan naka wanda kayi min alkawari". Adaidai wannan lokacin sai wani sabani ya faru atsakanin manyan Askarawan Mushrikan Makkah. Yayin da shi Utbatu bn Rabee'ah yake kokarin hana yin Yakin, yake kokarin kawai zai dauki fansa bisa dan uwan alkawarinsa wato Amru bn Alhadhramiy wanda Muminai suka kashe bisa kuskure, alokacin da suka fita wani Samame karkarin Sayyiduna Abdullahi bn Jahash. Har ya fara jan ra'ayin sauran mutanensu akan haka, da Abu Jahal ya samu labari sai yace masa "Kai dai Rago ne. Amma mu kan wallahi ba zamu koma gida ba, har sai Allah yayi hukunci tsakaninmu da Muhammadu". Ana cikin haka, Ashe su mushrikai Qishirwa ta fara cin addabarsu. Sai wani ...