FA'IDODIN TSAMIYA DAGA ZAUREN FIQHU
Tsamiya wata bishiya ce wacce ake shukata kuma ana magani da ita tun kusan shekaru dubu uku da suka gaba. Kuma ana samunta acikin dazuzzukan nahiyarmu ta Afirka da kuma kudancin nahiyar Asia. Likitocin Musulunci sun dade suna amfani da 'ya'yan bishiyar domin magance larurori masu yawa, haka kuma ana amfani da ita wajen hada nau'o'in abinci da abinsha. 'Ya'yan wannan bishiya ta tsamiya suna kunshe da sinadarai masu yawa sosai wadanda ke Qara ma jikin Dan Adam amfani mai yawa. Misali : - Vitamin A 151, Vitamin E, Vitamin B da kuma C. Sannan acikinta akwai Calcium, Potassium, thiamine, Tartaric Acid, Phosphorous, Proteins, Magnesium, Riboflavin. Haka kuma sabobbin ganyenta suna kunshe da sinadarin Sulfur da Calcium mai yawan gaske. Yanzu ga wasu fa'idodi ka'dan daga cikin dimbin abubuwan amfani dake cikin tsamiya : 1. CIWON ZUCIYA : Shan kunun tsamiya ko farau-farau (Juice) wanda aka yishi da tsamiya zai iya zama riga-kafi daga kamuwa da chutar hawan ...