ILLOLIN SHAN TABAR WEEWI
Acikin 'yan shekarun nan da matasa suka lalata kansu ta hanyar amfani da miyagun kwayoyi, Tabar Weewi ita ce kan gaba fiye da dukkan miyagun Kwayoyin da matasan suke amfani dasu. Wannan yasa ZAUREN FIQHU ya gudanar da bincike akanta domin ganowa irin illolinta, da kuma yadda take aiki wajen ruguza lafiyar jikin masu ta'ammali da ita. SUNAYENTA ************* Kasancewar ana amfani da ita kusan adukkan nahiyoyin duniya, wannan yasa Tabar Weewi take da sunaye kala-kala kamar haka: WEEWI, Ganye, Marijuana, Indian Hemp, Ganja, Pot, Igbo, Weed, Canabees, Hasheesh, Texas Tea, da dai sauransu. ILLOLINTA *********** Ganyen tabar WEEWI yana kunshe da Sinadarai sama da guda Arba'in masu chutar da lafiyar 'Dan Adam. Daga cikinsu har da sinadarin TETRA-HYDRO-CANNABINOL (T.H.C.) wani mummunan sinadari ne wanda yake chanza ma kwakwalwar 'Dan Adam yanayin yadda take karbar sakonni da yadda take sarrafa su. Duk lokacin da mashayin Weewi ya Zuki hayakinta, shi wannan Mummunan...