Posts

Showing posts with the label firdausi

SIFFOFIN ALJANNAH, DAGA ZAUREN FIQHU

An gina Aljannah ne da tubali (blocks) na Zinare da Azurfa tatacciya. Simintin cikinta anyishi ne da Almiski mai mutukar Qamshi. An cike tsakanin tubalanta da kayan ado na Zubarjadi da Yaaqootu. An halicci Qasar cikinta ne daga Za'afaran. Tana da Qofofi guda takwas kamar haka: 1. Jannatul Ma'awa. 2. Daarul Maqaam. 3. Daarus Salaam. 4. Daarul Khuld. 5. Jannatul 'Adni. 6. Jannatun Na'eem. 7. Jannatul Khaseef. 8. Jannatul Firdaus. JANNATUL MA'AWA ita ce daga Qasa, JANNATUL ADNI kuma ita ce matsakaiciya, JANNATUL FIRDAUSI kuma ita ce Qololuwa. Acikin Aljannah akwai Gonaki da lambuna wanda tsawon kowacce gona da fadinta ya kai tsawon tafiyar shekara 100 ko fiye da haka. Akwai bishiyoyi masu inuwa masu ni'ima da tsirrai marassa Qaya. An Halicci bishiyoyim cikinta ne daga madaukakin Zinare da tatacciyar Azurfa. Suna da manyan ganye kamar girman kunnen giwa, kuma 'ya'yan itacen bassu Qarewa. Suna nan nau'i-nau'i. Wadanda suke Qaunar juna ...