Posts

Showing posts with the label tafkin alkauthara

TAFKIN AL KAUTHARA

TAFKIN ALKHAUTHARA Yana daga cikin manyan abubuwan ni'ima na lahira wadanda Allah ya tanadar wa Annabinmu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) domin girmamawa gareshi da al'ummarsa. Acikin hadisai da dama Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yayi bayanin siffofin yadda tafkin yake, da kuma wadanda zasu sha daga gareshi. Misali hadisin Sayyiduna Abdullahi bn Umar (radhiyallahu anhuma) wanda yace Manzon Allah (saww) yace : "Tafkina (fa'dinsa) kamar nisan tsakanin Adanin da Amman, yafi Qankara sanyi, yafi zuma zaqi, kuma yafi dadin Qamshi fiye da Almiski. Kofunansa  kamar yawan taurari, wanda yasha daga gareshi ba zai Qara jin kishirwa ba har abada. Farkon mutanen da zasu fara gangarowa gareshi sune talakawan Almuhajirun. Sai wani yace "Su wanene Ya Rasulallah?!". Sai Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace "Sune wadanda gashin kansu yake da Qura-qura, fuskokinsu suke dauke da alamar wahala, tufafinsu yana da d...