GIRMAN KAI RAWANIN TSIYA!!!
JUBLAH BN AL-AIHAM wani Sarki ne daga sarakunan Yankin Ghassan. Hasken Musulunci ya ratsa zuciyarsa har ya Musulunta. Sannan sai ya rubuta wasika zuwa ga Khalifan Musulunci na wannan lokacin (Zamanin Sayyiduna Umar bn Al-Khattab ne -rta-) yana sanar dashi game da Musuluntarsa, kuma yana neman idan anyi masa izini zai zo har Birnin Madeena (wato Headquarter). Da Sayyiduna Umar (ra) ya karanta wasikar nan yayi farin ciki mutuka sosai. Hakanan sauran Jama'ar Musulman dake tare dashi (wato Sahabbai) duk sunyi Farinciki mai girma. Sai Sayyiduna Umar (ra) ya rubuta tasa wasikar zuwa gareshi cewa : "KAZO GAREMU. KANA DA IRIN HAKKIN DA DUK MUKE DASHI, KUMA DUK HAKKIN DAKE KANMU KAIMA YANA KAN KA". Shikenan sai ga Sarki Jublah ya taho tare da Sojoji dari biyar (500) akan dawakai suna yi masa rakiya. Yayin da suka kusanto Birnin Madeena sai Jublah ya tsaya ya chanza Tufafinsa. Ya sanya wasu Tufafin Sarauta irin na Qasaita.. Tufafi ne wadanda aka yi musu ado da Zinare, aka ci ba...