Posts

Showing posts with the label Soyayya

SHIN KA TA'BA ZUBDA HAWAYE DOMINSA KUWA?

An zageshi, an Jefeshi da duwatsu, Anyi masa jina-Jina Sahabbansa sun nemi yayi addu'a a hallakar da duniyar amma yace A'a. Maimakon haka ma sai addu'ar alkhairi yayi ma mutanensa. A lokacin da yaje ganawa da Ubangijinsa bai manta dani, da kai, da dukkan al'ummarsa ba. Sai da ya roka mana alkhairai masu yawa awajen Allah. Yayi Hijira daga Makkah zuwa Madeena. Sun biyoshi domin su kasheshi amma duk da haka bai yi musu mummunar addu'a ba.. Ya jure yunwa da Kishirwa da Zafi da sanyi duk domin al'ummarsa su samu shiriya. Aranar yakin Uhudu kafirai sunji masa rauni, amma duk da haka bai yi mummunar addu'a akansu ba. Saboda tausayi da Jin Qai irin nasa. Mutanen garin Ta'if sunyi masa wauta wacce ba'a ta'ba yin kamarta ba. Amma duk da haka bai Tsine musu ba, kuma bai yi mummunar addu'a akansu ba. Hakanan alokacin da zai bar duniya, Sai da ya tambayi Mala'ika Jibreelu ya gaya masa Alkawarurrukan da Ubangiji yayi ma al'ummarsa sannan ya...

MU SAN ANNABINMU (08)

Salati da aminci su tabbata bisa Annabin da ya zamanto matattarar lamarin halittu, Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa inuwar al'ummah da Sahabbansa da dukkan mabiyansa har zuwa ranar tashin halittu. HADUWARSU DA BUHAIRA : Yayin da Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya cika shekaru goma sha biyu aduniya, sai baffansa Abu Talib ya fara tafiye-tafiyen kasuwanci tare dashi. Kuma daga cikin safarorin da yayi dashi, akwai tafiyar da sukayi zuwa Birnin Sham (wato Syria). Yayin da suka iso wani gari mai suna Busra wanda ke kan hanyar Sham din, sai suka sauka domin hutawa awani waje, kuma anan ne wani Malamin addinin Nasaara (Kirista) mai suna Buhaira yaga Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Buhaira ya kasance yana yin ibadah ne tsawon shekaru acikin wajen bautarsa, anan ne ya hangi Manzon Allah (saww) kuma ya shaidashi ya gane cewa lallai shine Annabin Qarshe, ta dalilin wasu alamomi da ya gani. Misali ya lura da cewa Giza-gizai suna lullube wannan...

KUNDIN SOYAYYA (01)

Kar kuji na ambaci kalmar "Soyayya" kuyi zaton ko soyayyar wani ko wata nake nufi.. A'a ni ina nufin shiga cikin kundin soyayyar Masoyin Allah ne, Zababben Allah (saww) : Zamu leka cikin Kundin kaunarsa domin mu karanto wasu kalmomin Soyayya da yabo wadanda suka fito daga bakin Magabata na kwarai : 1. NANA KHADIJAH BNT KHUWAILID (RA) TA CE: "Da ache kowanne dare da rana zan samu shimfidar Annabi Sulaimanu (as) da kuma Mulkin Sarakunan Farisa, Qimarsu awajena ba zai kai koda fiffiken sauro ba.. In dai idanuna bai kasance yana kallon fuskarka ba". "Wallahi har abada Allah ba zai Wulakantaka ba". 2. HASSANU BN THABIT (RA) : "IDANUNA BASU TA'BA KALLON WANDA YAFIKA KYAWU BA. KUMA MATA BASU TA'BA HAIFUWAR WANDA YA FIKA KYAWU BA". "YAYIN DA NAGA HASKENSA YA BULLO, SAI DA NA SANYA HANNUNA AKAN IDONA SABODA KWARJINI". 3. IMAM ALIYU BN ABI TALIB (RA)  YACE: "BAN TA'BA GANIN WANI IRINSA KAFINSA BA. KUMA ABAYANSA MA B...