MADUBIN DUBAWA (067)
Wani labarin abin tsoro ne wanda ya faru tun zamanin Tabi'ai, Zauren Fiqhu ya bincikoshi domin ya zama abin lura garemu acikin rayuwarmu. Gashi nan kamar haka : Ibnu Abid Dunya ya ruwaito ta hanyar Umar bn Harun daga AbdulHameed bn Mahmud Almu'awwaly, yace : "Na kasance ina zaune awajen Abdullahi bn Abbas (Allah ya yarda dashi) sai ga wasu mutane sun zo wajensa suka gaya masa cewa : "Mun fito ne zamu je aikin Hajji akwai wani abokinmu tare damu. Sai da muka iso wani waje da ake kira "Zatus Sifahi" sai Allah ya karbi ransa. Mun gyarashi (wato munyi masa wanka mun sanya masa likkafani) mun je mun tona masa Qabari munyi masa lahdu (wato mun tona masa 'yar ciki din nan). Bayan mun kammala sai muka tarar da bakaken macizai sun cika Qabarin nasa fal!. Yayin da muka tona masa wani Qabarin dabam sai muka sake tarar da wasu macizan acikinsa shima.. Sai muka sake tona masa wani Qabarin, amma shima muka ga macizan sun cikashi, shine muka kyaleshi muka taho ...