Posts

Showing posts with the label Salami

DUWATSUN DAKE SONSHI (SAWW) - 1

DUWATSUN DAKE SONSHI (SAWW) 1 ************************************* Yana daga cikin Khasa'isu na Annabi Muhammadu (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) cewa Allah ya sanya soyayyarsa azukatan halittu masu motsi har ma marassa motsi. Mun kawo muku Qissar duwatsun dake yin gaisuwa gareshi tun tasowarsa agarin Makkah. Kuma mun gaya muku labarin wani dutsen dake gaisheshi bayan an fara yi masa wahayi. Sannan mun gaya muku Qissar da aka ruwaito daga Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib (rta) game da duwatsu da bishiyoyin dake yin gaisuwa ga Manzon Allah (saww). Daga cikin duwatsun duniya wadanda soyayyarsu ga Manzon Allah (saww) ta bayyana Qarara afili, dutsen Uhudu yana kan gaba.. Sayyiduna Anas bn Malik (ra) yace "Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya hau kan Dutsen Uhudu tare da Abubakar da Umar da Uthman (Radhiyallahu anhum). Sai dutsen yayi girgiza dasu (Saboda Shauqin jin tafin Qafar Manzon Allah akansa). Sai Manzon Allah (saww) ya bugeshi da Qafarsa mai ...