MU SAN ANNABINMU (19)
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM Salatai da amincin Allah Madaukaki su tabbata ga Fiyayyen Annabawansa, Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa da Sahabbansa da mabiyansa da mataimakansa har zuwa ranar sakamako. Wannan shine kashi na goma sha tara (19) acikin darasin tarihin Manzon Allah (saww) wanda ke zuwa muku daga Zauren Fiqhu Whatsapp. ISRA'I DA MI'IRAJI ****************** Shin menene ma'anar kalmar ISRA'I? : Ma'anarsa ita ce duk wata tafiya da aka yita acikin dare. Shi kuwa Mi'iraji ma'anarsa shine tafiya zuwa sama. Kuma wannan muhimmin al'amari ya faru ne agarin Makkah, kafin hijirah zuwa Madeena da shekara guda da rabi. Watarana sai ga Mala'ika Jibreelu yazo wajen Manzon Allah (saww) acikin dare tare da Buraqah. Wata dabba ce wacce keda jiki irin na doki kuma tana da kai irin na mutane, sannan tana da fukafukai ajikinta tana da tsananin saurin tafiya amma babu mai hawanta sai Annabawa alaihimus salam. Dabbar tana magana kamar yadda Dan Ad...