Posts

Showing posts with the label Karatu

DARAJOJIN AHLUL BAITI (ALAIHIMUS SALAM)

Wannan shine kashi na hudu acikin bayanin darajoji da falalar iyalan gidan Annabin Rahama (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) acikin jerin darussan Zauren Fiqhu : Sayyiduna Usamah 'dan Zaidu (rta) yace "Watarana na kwankwasa kofar gidan Annabi (saww) akan wasu bukatu, Sai (Naji yana cewa) : "WADANNAN 'YA'YANA NE, KUMA 'YA'YAN 'DIYATA. YA ALLAH NI INA SONSU KAIMA KASO SU KUMA KASO DUK MAI SONSU". (Imamut Tirmidhiy ne ya ruwaito). Imamu Muslim ya fitar da wani hadithi acikin Sahih nasa, juzu'i na 4 shafi na 1822. Da kuma Imamut Tirmidhiy acikin sunanu Juzu'i na 5 shafi na 128-128 dukkansu sun ruwaito ta hanyar Abu Juhaifah (Sahabin Annabi sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yana cewa: "Na kalli Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) sai naga lallai Alhasan 'dan Aliyu (Radhiyallahu anhuma) yana kama dashi". Hakanan an ruwaito ta hanyar Imamuz Zuhriy daga Sayyiduna Anas bn Malik (ra) yana cewa : "BABU...

FA'IDODIN YIN SADAQAH DAGA ZAUREN FIQHU

Ya kai 'Dan uwa Musulmi!! Ya ke 'Yar uwa Musulma!! Shin ko kun san cewa sadaqah tana da Mutukar amfani arayuwar 'Dan Adam? Bari kuji wasu daga cikin fa'idodin dake cikinta : 1. Sadaqah wata Qofa ce daga kofofin samun shiga Aljannah. 2. Acikin dukkan ayyukan lada, Sadaqah tana daga sahun gaba. Kuma mafificiyar sadaqah ita ce "Ciyar da abinci domin Allah". 3. Sadaqah tana inuwantar da Ma'abotanta aranar Alqiyamah, Kuma tana 'Yantar dashi daga shiga Wuta. (Gwargwadon yawan sadaqarka, shine gwargwadon ni'imar da zaka shiga aranar Alqiyamah). 4. Sadaqah tana bushe fushin Ubangiji. (Allah yana son masu yinta, don haka ba zai yi fushi da kai ba). 5. Sadaqah tana kiyaye mutum daga Azabar Qabari. 6. Sadaqah ita ce mafificiyar kyautar da zakayi ma Mamacinka. 7. Sadaqah, Ubangiji ne ke rainonta har sai ranar Alqiyamah za'a nuna maka ladanta. 8. Sadaqah tana tsarkake zuciya daga Qazantar nan ta rowa da kyashi. 9. Sadaqah tana janyo maka soyayyar ...

MAGANIN CIWON TSAKUWAR UWAR HANJI

TAMBAYA TA 2021 ******************** Assalamu alaikum Zauren Fiqhu, fatan alkhairi da godiya ga Malam. Ni dalibi ne a wannan zaure mai albarka na shafin facebook, Ina fama da wani irin ciwon ciki ne wanda idan ya rike ni ko tashi tsaye inyi tafiya mai kyau bana iyawa, kuma nayi scanning har sau uku amma ba komai take nunawa ba, sai yau danayi awani asibitin sukayi confirming appendixes ne. Don  Allah Malam ban Sani ba ko akwai wasu magungunan da zan iya amfani dasu Wanda ba sai anyimin operation ba. JAZAKUMALLAH BI AHSANUL KHAIR. AMSA ******* Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Da farko dai muna yi maka fatan alkhairi da fatan Allah ya baka lafiya daga dukkan abinda ke damunka. Akwai abubuwa da dama a likitancin Musulunci wadanda sukan magance irin wannan ciwon in sha Allahu. Kamar yadda bayanai suka gabata anan Zauren Fiqhu. Ga wasu nan kamar haka : 1. Ka samu Garin Kustul Hindi cokali 7, garin Shammar cokali 7, Garin Habbatus sauda cokali 7, garin Kirfa coka...