Posts

Showing posts with the label zikiri

DUNIYAR ALJANU DA ABINDA TA KUNSA (KASHI NA 1)

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM ************************************ DON ALLAH IDAN KANA DA SAURIN TSORATA/FIRGITA, KAR KA KARANTA.. Mun gabatar da karatun ne a ZAUREN FIQHU WHATSAPP (3). Kuma ga yadda karatun ya kasance: Duniyar Aljanu wata irin duniya ce wacce ta bambanta sosai da tamu duniyar. Ta wajen Kamanninta, da yanayinta, da kuma abubuwan da ta Qunsa. Allah ya halicci Aljanu bisa siffofi nau'i uku kamar yadda Manzon Allah (saww) ya fada acikin wani hadisi. Acikinsu akwai wadanda suke da Jikinsu shigen irin namu. Sai dai bambancin yanayin Qirar jikin da kuma girman halittar. Akwai kuma wadanda Allah ya haliccesu ne abisa siffar Karnuka da Macizai. (Wadannan sune wadanda idan suna jikin mutum zai rika yawan mafarkin Karnuka ko Macizai, ko Qadangaru, etc). Akwai kuma wadanda su acikin dazuzzuka suke yin rayuwarsu. Sai dai basu zama waje guda. Suna yawan tashi ne daga wani wajwn zuwa wani. Duk wadannan abubuwan da nake fada, sun samo asali ne daga Alqur'ani da Hadisan...

FALALAR FA'DAR LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHI

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI : Salati da amincin Allah su tabbata bisa Shugaban Annabawa da Manzanni, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa da Sahabbansa da Masu binsu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako. Wannan bayani ne game da falalar "LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHIL ALIYYIL AZEEM". Kasancewar muna yawan bada shawarar arika yawaita yinta, acikin fatawoyinmu na Zauren Fiqhu, shi yasa naga zai yi kyau mu fa'di falalarta sosai yadda mutane zasu ji su Qaru, kuma su riketa sosai. Sayyiduna Abu Musal Ash'ariy (Allah ya yarda dashi) yace "Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata gareshi) yace mun "KACE LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAH DOMIN HAKIKA ITA TASKA CE DAGA TASKOKIN ALJANNAH". To kunga ashe kenan yawaita fa'darta zai iya zama dalilin samun waccen taskar ta lahira, tare da rahamar Allah. Sannan kuma ya wadata mutum tun daga nan duniya. Mak'hul (rah) daya daga cikin magabata na kwarai yace "Duk wanda yace...

DAGA TASKAR AHLUL BAITI (ALAIHIMUS SALAM)

IMAM JA'AFAR ASSADIQ (RTA) YACE: "Ina mamakin mutumin da yake cikin tsoro amma bai dukufa cikin karanta "HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKEEL" ba. Ina mamakin mutumin da Bakin ciki ya dameshi amma bai karanta "LA ILAHA ILLA ANTA SUB'HANAKA INNEE KUNTU MINAZ ZWALIMEENA" ba. "Ina mamakin Mutumin da Masu Makirci suka dameshi da Makirci amma bai karanta "WA UFAWWIDHU AMREE ILAL LAAH. INNAL LAAHA BASEERUN BIL 'IBAADI' ba". Ni kuma Mai Zauren Fiqhu na Qara da cewa : "Ina mamakin mutumin da yake fama da wata jinya ko rashin lafiya, amma bai yawaita karanta "ANNEE MASSANIYADH DHURRU WA ANTA ARHAMUR RAHIMEENA' ba". "Ina mamakin mutumin da yake neman haihuwa amma bai yawaita "RABBEE HABLEE MIN LADUNKA DHURRIYYATAN TAYYIBAH, INNAKA SAMI'UD DU'A'I ba". "Ina mamakin mutumin da talauci ya dameshi amma bai yawaita Istighfari da Salatin Annabi (saww) ba. Ina mamakin mutumin da ya shiga mats...

ZIKIRINMU NA YAU (25/10/2017)

ZIKIRINMU NA YAU (25/10/2017) ********************************* Hadithi daga Ɗalqu bn Habeeb yace "Wani mutum yazo wajen Abud Darda'i (rta) yace masa "Ya kai Abud Darda'i! Hakika gidanka ya Qone!". Sai Abud Darda'i yace "A'a bai Qone ba! Allah ba zai ta'ba yin haka ba, saboda wasu kalmomi da najisu daga wajen Manzon Allah (saww). Duk wanda ya fa'desu a farkon wuni, babu wata musibar da zata sameshi har sai ya yammanta. Kuma duk wanda ya fa'desu a Qarshen wuni, babu wata musibar da zata sameshi har sai ya wayi gari : اللهم أنت ربي لا إله إلا أنت ، عليك توكلت وأنت رب العرش العظيم.  ما شاء الله كان وم...