LABARIN UMMU MALIK (RTA)
Akwai Wata Mata mai suna Ummu Malik ta kasance tana hidimta ma Manzon Allah (saww). Watarana ta zuba Man girki acikin Salka sannan ta tafi dashi ta kai masa (saww). To rannan ta wayi gari batta da Man gyadan ya Qare. Kuma gashi 'Ya'yanta suna bukatarsa zasu ci abinci. Da taje ta dauko Salkar sai ta tarar da ita acike Fal da man gyada. Ta dauko ta bama yaranta suka ci abinci dashi.. Ta kasance duk lokacin da take bukatar Mai agidanta, da ta dauko salkar sai ta tarar da ita acike Gal da mai. Rannan kawai sai ta juye man, ta tatse Salkar gaba daya... Tun daga ranar sai ta deba ganin Komai acikin salkar. Don haka taje ta sanar da Manzon Allah (saww). Sai yace mata : "DA ACHE BAKI TATSESHI BA, DA SAI YA ISHEKI HAR TSAWON RAYUWARKI". Acikin wata ruwayar kuma ance da ta koma gida sai taga Salkar man gyadar kamar ba'a juye ba. Don haka sai hankalinta ya tashi. Ta dawo wajen Manzon Allah (saww) Tace masa "Ya Rasulallahi ko an saukar da wata ayah. e game dani?...