Posts

Showing posts with the label Makkah

MU SAN ANNABINMU (02)

MAHAIFANSA : Mahaifinsa shine Abdullahi 'dan AbdulMuttalibi 'dan Hashim. Yana daga mafiya kyawu da nagartar samarin zamaninsa. Mahaifiyarsa kuwa ita ce Nana Ãminatu (Az-Zuhriyyah) 'yar Wahbin 'dan Abdu Manaf 'dan Zuhrata. Ta fito daga dangi masu tsarki da nagarta da daukaka daga cikin dangogin larabawa Quraishawa. HAIHUWARSA : An haifi Shugabanmu Annabi Muhammadu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ne a garin Makkah acikin unguwar banu Hashim, ranar litinin sha biyu (12) ga watan rabee'ul awwal ashekarar giwaye, wacce tazo daidai da 20 ga watana aprilu shekara ta 571 miladiyyah. An haifeshi ne maraya kasancewar mahaifinsa ya riga ya rasu tun yana da 'yan watanni acikin mahaifiyarsa. Kuma an haifeshi mai tsarki mai haske mai Qamshi, idonsa da tozali. Kuma ya sauka tare da haske mai girma wanda ya haskake garin makkah baki dayansa har garuruwa masu nisa. Kakansa Abdul Muttalibi ne ya ra'da masa wannan suna "MUHAMMADU" bisa ilhamar Ubang...

MU SAN ANNABINMU (07)

Assalamu alaikum. Wannan shine darasi na bakwai acikin tarihin Shugaban Halitta (saww) kamar yadda muka gabatar a Zauren Fiqhu Whatsapp. ZAMANSA AWAJEN BAFFANSA : Kamar yadda muka fa'da tun da farko, bayan rasuwar Kakansa sai Annabi Muhammadu (saww) ya koma hannun baffansa mai suna Abu Talib wato dan uwan mahaifinsa wanda suka fito ciki daya. Alokacin nan yana da shekaru takwas (8) kenan aduniya. Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya taso ahannun Abu Talib cikin soyayya da mutuntawa da girmamawa, har zuwa lokacin da yayi masa aurensa na fari. Ya zauna awajensa tare da sauran yaran gidan kuma shi yayi fiche wajen kyawun halaye da dabi'u. Ba ya yin wasa ko hayaniya irin wacce sauran yara sukeyi. Haka kuma wajen cin abinci ba ya ha'dama irin wacce yara keyi. Yana cin abinda ke gabansa ne ka'dai, kuma da zarar yaci ka'dan ya isheshi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). SANA'O'INSA (SAWW)  : Ya fara sana'a ne tun yana da shekaru takwas...

MU SAN ANNABINMU (09)

Da Sunan Allah Mai rahama mai jin kai. Salati da amincinsa su tabbata bisa Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa da Sahabbansa da dukkan Magoya bayansa. Wannan shine darasu na 9 acikin tarihin Shugaba (saww) wanda ke zuwa muku daga Zauren Fiqhu Whatsapp. HARBUL FUJJAR ****************** Bayan Annabi Muhammadu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya cika shekaru ashirin (20) aduniya, wani Yaqi ya barke atsakanin Larabawa. Wato Quraishawa da Banu Kinanah ne suka ha'du suka yaqi wata Qabila mai suna "Qaisu 'Eelan". Annabi (saww) ya halarci wajen wannan yaqin alhali yana matashi, yaje tare da baffaninsa 'ya'ysn Abdul Muttalib yana kawo musu kibiyoyin harbi. Amma dai daga karshe yaqin ya Qare da sulhu atsakanin Qabilun. An kira wannan yaqin da sunan "Harbul Fujjar" ne saboda an yishi ne acikin watanni masu alfarma, wadanda ba'a saba yin yaqi acikinsu ba. HILFUL FUDHUL Bayan kammala Yaqin nan na Harbul Fujjar sai Quraishawa suka ha...