MU SAN ANNABINMU (09)
Da Sunan Allah Mai rahama mai jin kai. Salati da amincinsa su tabbata bisa Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa da Sahabbansa da dukkan Magoya bayansa. Wannan shine darasu na 9 acikin tarihin Shugaba (saww) wanda ke zuwa muku daga Zauren Fiqhu Whatsapp. HARBUL FUJJAR ****************** Bayan Annabi Muhammadu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya cika shekaru ashirin (20) aduniya, wani Yaqi ya barke atsakanin Larabawa. Wato Quraishawa da Banu Kinanah ne suka ha'du suka yaqi wata Qabila mai suna "Qaisu 'Eelan". Annabi (saww) ya halarci wajen wannan yaqin alhali yana matashi, yaje tare da baffaninsa 'ya'ysn Abdul Muttalib yana kawo musu kibiyoyin harbi. Amma dai daga karshe yaqin ya Qare da sulhu atsakanin Qabilun. An kira wannan yaqin da sunan "Harbul Fujjar" ne saboda an yishi ne acikin watanni masu alfarma, wadanda ba'a saba yin yaqi acikinsu ba. HILFUL FUDHUL Bayan kammala Yaqin nan na Harbul Fujjar sai Quraishawa suka ha...