Posts

Showing posts with the label hadiyyah

SHIN KA TA'BA ZUBDA HAWAYE DOMINSA KUWA?

An zageshi, an Jefeshi da duwatsu, Anyi masa jina-Jina Sahabbansa sun nemi yayi addu'a a hallakar da duniyar amma yace A'a. Maimakon haka ma sai addu'ar alkhairi yayi ma mutanensa. A lokacin da yaje ganawa da Ubangijinsa bai manta dani, da kai, da dukkan al'ummarsa ba. Sai da ya roka mana alkhairai masu yawa awajen Allah. Yayi Hijira daga Makkah zuwa Madeena. Sun biyoshi domin su kasheshi amma duk da haka bai yi musu mummunar addu'a ba.. Ya jure yunwa da Kishirwa da Zafi da sanyi duk domin al'ummarsa su samu shiriya. Aranar yakin Uhudu kafirai sunji masa rauni, amma duk da haka bai yi mummunar addu'a akansu ba. Saboda tausayi da Jin Qai irin nasa. Mutanen garin Ta'if sunyi masa wauta wacce ba'a ta'ba yin kamarta ba. Amma duk da haka bai Tsine musu ba, kuma bai yi mummunar addu'a akansu ba. Hakanan alokacin da zai bar duniya, Sai da ya tambayi Mala'ika Jibreelu ya gaya masa Alkawarurrukan da Ubangiji yayi ma al'ummarsa sannan ya...