Posts

Showing posts with the label Annabi Muhammadu

HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (114)

HAKURIN RIKON YARA MATA : ****************************** Hadisi daga Sayyiduna Abu Hurairah (Allah ya yarda dashi) daga Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yana cewa : "DUK WANDA YAKE DA 'YA'YA MATA GUDA UKU, KUMA YAYI HAKURI BISA JIBINTAR LAMARINSU, DA BAQIN CIKINSU DA FARIN CIKINSU, ALLAH ZAI SHIGAR DASHI ALJANNAH SABODA JIN QANSA GARESU". Sai wani mutum yace "Ya Rasulallahi koda guda biyu ne?". Sai Annabi (saww) yace masa "KODA GUDA BIYU NE". ADUBA : AT-TARGHEEB WAT TARHEEB (Juzu'i na 3 shafi na 47). QARIN BAYANI *************** Allah madaukakin sarki ya sanya falala mai yawa cikin rikon 'diya mata da tarbiyyarsu fiye da yadda ya sanya acikin rikon 'ya'ya maza. Ba don komai sai saboda irin yadda muhimmancinsu yake acikin al'ummah. Misali : 'Ya mace guda idan ta samu cikakkiyar kulawa tare da tarbiyyah ingantacciya tana iya tarbiyyantar da 'ya'yanta har na makobta har shi kansa Maigidan...

MU SAN ANNABINMU (05)

RASUWAR MAHAIFIYARSA MAI GIRMA (SAWW) : Bayan Mala'ikun nan sun kwantar dashi sun tsaga kirjinsa, sai Halimatus Sa'adiyyah ta dawo dashi wajen mahaifiyarsa saboda jin tsoron da takeyi bisa lafiyarsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Bayan dawowarsa wajen Mahaifiyarsa da shekaru biyu wato lokacin yana da shekara shida kenan aduniya, sai tayi nufin ta ziyarci garin Yathrib (Madeenah) wajen kawunnanta Banun Najjar, da kuma Qabarin mijinta Abdullahi. Ta tafi tare da Manzon Allah (saww) tayi wadannan ziyarori, amma akan hanyarta ta dawowa sai jinyar ajali ta kamata, kuma ta rasu adaidai wani waje da ake kira "ABWA'U" kuma anan aka binneta, Qabarinta yana nan har yanzun nan. Shikenan Manzon Allah (saww) ya zamanto cikakken maraya ta bangaren mahaifansa baki daya. To alokacin nan akwai baiwar mahaifinsa wacce ake kiranta "Ummu Aymana - Barakatul Habashiyyah" ita ta kamo hannunsa suka dawo garin Makkah,  kuma shekarunsa shida awannan lokacin. ALLAHU...

MU SAN ANNABINMU (06)

KOMAWARSA HANNUN KAKANSA MAI DARAJA (SAWW)  : Daga nan sai ya koma hannun Kakansa wato mahaifin mahaifinsa, mai suna Abdul Muttalibi 'dan Hashim. Ya kasance mai nuna so da Qauna ga wannan jikan nasa mai daraja (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Ya kasance duk inda zai je tare suke tafiya, ba ya yin barci sai tare dashi, hakanan wajen cin abinci ma. Kuma yasoshi fiye da sauran jikanunsa da 'ya'yansa. Ya kasance yana girmama Annabi (saww) kuma yana gaya ma mutane cewa "Akwai wani babban lamari da zai faru ga jikan nan nawa". Sai dai zamansu bai tsawaita ba, domin bayan shekaru biyu kachal sai shima ya rasu,  Kuma yabar wasiyyah ga 'daya daga cikin 'ya'yansa mai suna "Abu Talib" cewa shi zai ci gaba da kulawa da wannan jikan nasa, Annabi Muhammadu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Salati da amincin Allah si tabbata bisa Annabin Rahma Ma'abocin tausayi da karamci, tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da mabiyansa ...

SHIN KA TA'BA ZUBDA HAWAYE DOMINSA KUWA?

An zageshi, an Jefeshi da duwatsu, Anyi masa jina-Jina Sahabbansa sun nemi yayi addu'a a hallakar da duniyar amma yace A'a. Maimakon haka ma sai addu'ar alkhairi yayi ma mutanensa. A lokacin da yaje ganawa da Ubangijinsa bai manta dani, da kai, da dukkan al'ummarsa ba. Sai da ya roka mana alkhairai masu yawa awajen Allah. Yayi Hijira daga Makkah zuwa Madeena. Sun biyoshi domin su kasheshi amma duk da haka bai yi musu mummunar addu'a ba.. Ya jure yunwa da Kishirwa da Zafi da sanyi duk domin al'ummarsa su samu shiriya. Aranar yakin Uhudu kafirai sunji masa rauni, amma duk da haka bai yi mummunar addu'a akansu ba. Saboda tausayi da Jin Qai irin nasa. Mutanen garin Ta'if sunyi masa wauta wacce ba'a ta'ba yin kamarta ba. Amma duk da haka bai Tsine musu ba, kuma bai yi mummunar addu'a akansu ba. Hakanan alokacin da zai bar duniya, Sai da ya tambayi Mala'ika Jibreelu ya gaya masa Alkawarurrukan da Ubangiji yayi ma al'ummarsa sannan ya...

MU SAN ANNABINMU (08)

Salati da aminci su tabbata bisa Annabin da ya zamanto matattarar lamarin halittu, Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa inuwar al'ummah da Sahabbansa da dukkan mabiyansa har zuwa ranar tashin halittu. HADUWARSU DA BUHAIRA : Yayin da Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya cika shekaru goma sha biyu aduniya, sai baffansa Abu Talib ya fara tafiye-tafiyen kasuwanci tare dashi. Kuma daga cikin safarorin da yayi dashi, akwai tafiyar da sukayi zuwa Birnin Sham (wato Syria). Yayin da suka iso wani gari mai suna Busra wanda ke kan hanyar Sham din, sai suka sauka domin hutawa awani waje, kuma anan ne wani Malamin addinin Nasaara (Kirista) mai suna Buhaira yaga Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Buhaira ya kasance yana yin ibadah ne tsawon shekaru acikin wajen bautarsa, anan ne ya hangi Manzon Allah (saww) kuma ya shaidashi ya gane cewa lallai shine Annabin Qarshe, ta dalilin wasu alamomi da ya gani. Misali ya lura da cewa Giza-gizai suna lullube wannan...

MU SAN ANNABINMU (SAWW) - 1

NASABARSA : ************** Shine Shugabanmu Muhammadu 'dan Abdullahi 'dan Abdul Muttalibi 'dan Hashim 'dan Abdu Manafi 'dan Qusayyu 'dan Kilabu 'dan Murratu 'dan Ka'abu 'dan Lu'ayyu 'dan Ghalibu 'dan Fihru 'dan Maliku 'dan Nadhru 'dan Kinanatu 'dan Khuzaimah 'dan Mudrikah 'dan Ilyas 'dan Mudhar 'dan Nizaar 'dan Ma'addu 'dan 'Adnan shi kuma Adnan yana daga cikin jikokin Annabi Isma'il (as) shi kuma 'dan Annabi Ibraheem (as). Nasabah ce tsarkakakkiya wacce babu wani datti ko Qazanta irin ta zamanin jahiliyyah da ta ta'ba ratsata. Kowanne daga cikin iyayensa da kakanninsa tsarkakakke ne kuma mafi nagartar mutanen zamaninsa. Haka kuma iyayensa mata dukkaninsu tsarkaka ne madaukaka acikin jama'ar zamunnansu. Shi da kansa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace " NI ZA'BABBE NE DAGA CIKIN ZABABBU DAGA CIKIN ZABABBU ". Allah ya zabi zuriyar gidan...

MAGANARSA DA DABBOBI (SAWW) 07

Alqadhy 'Iyadh bn Musa Alyahsubiy (Allah ya rahamsheshi) ya ruwaito acikin littafinsa Mai albarka (Ash-Shifa) aciki Qissar makiyayin dabbobin nan wanda kura tayi magana dashi, mutumin yana cikin tsananin mamaki sai kurar tace masa "Ai kai ne babban abun mamaki.. Kana tsaye akan tumakinka kuma ka bar wannan Annabin wanda Allah bai ta'ba aiko Annabin da ya fishi girma ba (baka je ka bada gaskiya dashi ba). "Kuma yana da daraja awajen Allah tunda har an bude masa Qofofin Aljannah kuma ga 'Yan Aljannar nan an bude musu suna kallon Yaqin Sahabbansa. Babu abinda ke tsakaninka dashi sai wannan Surkukin. (Kaje kayi imani dashi) Sai kaima ka zamto acikin rundunar Allah". Sai shi Makiyayin yace mata "To wa zai kula min da tumaki na?". Sai tace "Ni zan kula maka dasu har sai ka dawo". Sai ya sallamar da dabobinsa ga Kurar, kuma ya tafi yaje ya tarar da Manzon Allah (saww) awajen Yaqi, ya bashi labarin dukkan avidna ya faru tsakaninsa da kurar, ku...

SHAUKIN SON MA'AIKI (SAWW) DAGA KUTUTTUREN DABINO

Image
Acikin jerin Mu'ujizozin Manzon Allah (saww) wadanda Zauren Fiqhu ke kawowa, in sha Allahu yau zamuyi magana akan Shahararriyar Mu'ujizar nan wacce duniya take labari. Wato Kukan da itacen dabino (Kututture) yayi saboda shauki, da kuma tashin hankalin da yaji yayin rabuwa da Ma'aiki (saww). Hadisi daga Sayyiduna Jabir bn Abdillahil Ansariy (ra) yace : Manzon Allah (saww) ya kasance ranar Juma'a yana tsayawa ajikin wata bishiya ko itacen dabino (Idan zai yi Khutbah). Sai wata Mace ko Namiji daga cikin mutanen Madeenah tace "Ya Rasulallahi ko mu sanya maka Mimbari ne?". Sai Manzon Allah (saww) yace: "IDAN KUN SO". Don haka sai suka sanya masa Minbari. Yayin da ranar Juma'a tayi, Manzon Allah (saww) ya tafi zuwa ga Minbarin, Sai wannan itacen dabinon yayi kururuwa irin Kururuwar da Jariri ke yi. Sai Manzon Allah (saww) ya sauko (daga kan Minbarin) yaje ya rungumeshi. Sai ya rika yi wani abu kamar yadda yaro Qarami keyi idan an rarrasheshi. Sai...

ALLAH YAFI GABAN KWATANCE

Hakika Allah Madaukakin Sarki, Samamme ne tun gabannin samuwa. Kuma dawwamamme ne ba tare da farko ko Qarshe ba. Babu Jihar da take ritsashi, kuma babu wajen da ake rasashi. Shi Makadaici ne wanda Qirge ko lissafi basu riskarsa. Yafi gaban kwatance da zuciya ko tunanin masu tunani. Bai haifa ba, kuma ba'a haifeshi ba. Shine abin nufin dukkan halittu. Kuma babu wani kini agareshi. Bai yi kama da komai ba, kuma babu abinda yayi kama dashi. Shi Mawadaci ne ba ya bukatar komai awajen kowa, shine wanda kowa ke bukatar komai awajensa. Mai cikakken iko ne wanda ikonsa bai rataya da zamani ko makani ba. Kuma mai nufi ne ga dukkan abinda yaso. Babu mai tambayarsa akan abinda yayi, kuma babu mai tuhumarsa akan abinda bai so kasantuwarsa ba. Shi Masani ne tun gabannin komai. Shi yasan komai, kuma ya san kowa. Amma babu wanda ya sanshi sai shi kansa. Shi Rayayye ne tun gabannin dukkan rayayyu. Kuma shi rayayyen bayan macewar dukkan rayayyu. Rayuwarsa bata ratayu da komai ba. Kuma bata do...

ZUWA GA MASOYIN RAINA (SALLAL LAAHU ALAIHI WA AALIHI WA SALLAM)

Amincin Allah ya tabbata agareka gwargwadon matsayinka awajen Ubangijinka Ya Masoyin Allah. Hakika Ni na shaida cewa Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, kuma shi kadai ya chanchanta a bauta masa. Kuma na shaida Kai Bawansa ne kuma Manzonsa ne. Ya aikoka alokacin da dukkan wani hasken shiriya ya riga ya dusashe. Gaskiya tayi Qas, sai Qarya take hankoro. Kazo da haskenka ka kauda dukkan Qarya da ma'abotanta. Ka isar da aiken Allah, Ka karya Gumaka ka tsarkake Bautar Allah. Ka fidda bayi daga Kafirci zuwa ga Imani, daga jahilci zuwa ga Ilimi, daga Zalunci zuwa ga adalci. Hakika na shaida cewa cikin dukkan bayin Allah babu tamkarka babu kamarka. Kai ne Shugaban dukkan bayin Allah. Kai ne Haskensu kuma da kai Allah ya haskakasu. Kai ne Shugaba kuma jagoran dukkan Annabawa da Manzannin Allah. Kuma kai kadai ne wanda saboda kai Allah ya tara dukkan Annabawa da Manzanni sai da sukayi Imani dakai, Suka dauki alkawarin cewa su Mataimakanka ne, zasu taimakeka akan aikinka sanna...

RANAR DA BABU KOKWANTO

Image
'Dora hannunka akan Qirjinka... Zakaji yadda zuciyarka take bugawa, babu dare babu rana.. tana tafiya ne bisa wani Saiti na musamman wanda Ubangijinka yayi mata tun asali. Nisan tafiyar wannan saitin shine Gwargwadon nisan ajalinka. Kuma Ubangijinka yana sane da yawan adadin bugawar da yayi izini agareta. Idan lokacinta ya cika, ba zata jinkirta maka ba, Ba zata Qara motsi ba. Ranar da Mala'ikan numfashinka da Mala'ikan abincinka, da Mala'ikan abin shanka zasu zo suyi bankwana dakai, suce maka dukkan rabonka na duniyar nan ya riga ya Qare. Ranar da Iyayenka da 'Yan uwanka da iyalanka zasu kewayeka, amma ba zasu amfana maka komai ba... Ba zasu hana abinda zai sameka ya sameka ba, kuma ba zasu sanya ajinkirta maka ba, kuma ba zasu sanya a saukaka maka ba. Wallahi duk wannan kururuwar da sukeyi TA QARYA CE! Suna yin kuka ne don tsoron halin da zasu shiga bayan rasuwarka. Amma ba wai sunayi ne domin tausaya maka akan halin da zaka shiga ba.. Kuma WALLAHI duk cikin...