Posts

Showing posts with the label kirari

GUZURIN SAFIYA (01)

Ya Ubangiji hakika mun wayi gari muna masu imani da kadaitakarka, da kuma Manzancin Annabinka Muhammadu (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam). Muna cikin masu mika godiya da kirari gareka bisa dukkan ni'imominka na fili da boye.. Hakika bamu isa mu gode maka da irin godiyar da ta chanchanta gareka ba. Muna cikin masu dogaro dakai da kuma neman taimakonka.. Hakika Kaine Fiyayyen Majibinci, Fiyayyen Mataimaki, Kuma fiyayyen abin dogaro. Hakika Kaine Mai yin baiwa ga bayinka ba don sun chanchanta da ita ba, sai dai don falalarka da rahamarka garesu. To Ya Allah muna Kamun Qafa da fiyayyen Masoyinka, da dukkan abinda yafi soyuwa gareka, Ka cika ni'imominka akanmu, Ka bamu lafiyar fili da boye, Ka suturcemu da bargon suturarka, Kayi mana arzikin duniya da lahira. Ameen. Salatinka mafi girma da amincinka mafi cika su tabbata ga Fiyayyen Bayi,  Annabi Muhammadu kenan tare da iyalan gidansa hasken al'ummah, da Sahabbansa taurarin shiriya, da dukkan Salihan bayinka har zuwa...

ALLAH YAFI GABAN KWATANCE

Hakika Allah Madaukakin Sarki, Samamme ne tun gabannin samuwa. Kuma dawwamamme ne ba tare da farko ko Qarshe ba. Babu Jihar da take ritsashi, kuma babu wajen da ake rasashi. Shi Makadaici ne wanda Qirge ko lissafi basu riskarsa. Yafi gaban kwatance da zuciya ko tunanin masu tunani. Bai haifa ba, kuma ba'a haifeshi ba. Shine abin nufin dukkan halittu. Kuma babu wani kini agareshi. Bai yi kama da komai ba, kuma babu abinda yayi kama dashi. Shi Mawadaci ne ba ya bukatar komai awajen kowa, shine wanda kowa ke bukatar komai awajensa. Mai cikakken iko ne wanda ikonsa bai rataya da zamani ko makani ba. Kuma mai nufi ne ga dukkan abinda yaso. Babu mai tambayarsa akan abinda yayi, kuma babu mai tuhumarsa akan abinda bai so kasantuwarsa ba. Shi Masani ne tun gabannin komai. Shi yasan komai, kuma ya san kowa. Amma babu wanda ya sanshi sai shi kansa. Shi Rayayye ne tun gabannin dukkan rayayyu. Kuma shi rayayyen bayan macewar dukkan rayayyu. Rayuwarsa bata ratayu da komai ba. Kuma bata do...

ANNABINA SHUGABANA MACECINA (SAWW)

Image
ANNABINA, MASOYINA (SAWW) SHINE : ***************************************** DHU QUWWATIN : Ma'abocin Qarfin jiki da Qarfin Hujjah. Annabin da shi kadai yaci nasarar da sauran Annabawan Allah vasu samu ba. Ya kori shirka,  ya karya gumaka, ya tsarkake Ka'abah. DHU HURMATIN : Ma'abocin alfarma aduniya da lahira. Annabin da saboda shi Allah yake dauke Bala'i, kuma yake saukr da niimah.  Shine wanda saboda alfarmarsa al'ummarsa ta samu daukaka da darajoji. DHU MAKANATIN : Ma'abocin Qurewar Matsayi afadar Allah. Shine wanda Allah ya tara dukkan Annabawa sukayi imani dashi, sukayi masa chaffa, Suka dauki alkawarin taimakonsa wajen isar da sako. DHU 'IZZIN : Ma'abocin Buwaya aduniya da lahira. Shine wanda ya chusa tsoro da razana azukatan Sarakunan duniya tun afarkon lokacin bayyanarsa. DHU FADHLIN : Ma'abocin Falala da fifiko a saman dukkab halittu. Shine wanda ambaton sunansa yake yaye damuwa ga Masoyansa. Kallon fuskarsa yakan Gigita hankali,  Tun...