Posts

Showing posts with the label yakin Badar

MU SAN ANNABINMU (25)

Da sunan Allah mai rahama mai jin qai, salati da amincin Allah su tabbata bisa Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa shiryayyu. YAQIN BANU QAINUQA'A : Banu Qainuqa'a sunan wata Qabila ne daga cikin Qabilun yahudawan madeenah wadanda Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya qulla alkawarin zan lafiya dasu tun farkon zuwansa garin. Nasarar da Manzon Allah (saww) ya samu a yaqin badar ta basu haushi, don haka sai suka fito fili suna bayyana qiyayyarsu ga Musulmai da kuma soyayyarsu ga mushrikan Quraishawa. Kuma sun kasance suna gadara da Qarfin tattalin arziki kasancewarsu masu sana'ar zinare ne. Suna cin mutuncin jama'ar musulmai, suna yi musu izgili har dai watarana suka yiwa wata mace musulma tsirara a kasuwarsu, ta nemi taimako awajen wani musulmi ya taimaka mata ya kashe bayahuden da ya zalunceta. Sai sauran yahudawan suka taru akansa (shi Musulmin) suka kasheshi. Wannan shine tushen yaqin. Kuma Manzon Allah (sa...

QISSAR YAQIN BADAR KASHI NA TARA

AN FARA GWABZAWA TSAKANIN JARUMAI Acikin kashi na takwas mun tsaya ne adaidai wajen da Kowanne bangare sukayi sahu sahu, kuma Manzon Allah (saww) yayi addu'a yana cewa: "Ya Allah Ga Quraishawa nan sun tunkaro da Alfaharinsu, suna jayayya da kai, kuma suna Qaryata Manzonka.. Ya Allah taimakon nan naka wanda kayi min alkawari". Adaidai wannan lokacin sai wani sabani ya faru atsakanin manyan Askarawan Mushrikan Makkah. Yayin da shi Utbatu bn Rabee'ah yake kokarin hana yin Yakin, yake kokarin kawai zai dauki fansa bisa dan uwan alkawarinsa wato Amru bn Alhadhramiy wanda Muminai suka kashe bisa kuskure, alokacin da suka fita wani Samame karkarin Sayyiduna Abdullahi bn Jahash. Har ya fara jan ra'ayin sauran mutanensu akan haka, da Abu Jahal ya samu labari sai yace masa "Kai dai Rago ne. Amma mu kan wallahi ba zamu koma gida ba, har sai Allah yayi hukunci tsakaninmu da Muhammadu". Ana cikin haka, Ashe su mushrikai Qishirwa ta fara cin addabarsu. Sai wani ...

YAU CE RANAR YAKIN BADAR

Wannan rana ta 18 ga Ramadhan tana daga cikin ranakun tarihi wadanda bai kamata duk wani musulmi ya manta dasu ba. Kamar shekaru 1434 da suka gabata, awannan ranar kafiran Makkah suka fito da manyan Jarumansu da Manyan Masu Hannu da shuninsu.. Gaba dayansu su 1000 (dubu daya). Duk sun fito da kayan yakinsu sun taho domin su Murkushe Musulmai da Musulunci. Shi kuma ANNABI (saww) ya fito tare da Sahabbansa 'yan kadan, su 313 ne. Kuma babu wani cikakken shirin Yaki ko manyan Makamai sosai tare dasu.. Daga Bangaren Dakarun Kafirai akwai manyan kwamandodi irin su: - A bu Jahal bn Hisham . - Shaibatu Bn Rabee'ah . - Utbatu Bn Rabee'ah . - Umayyatu bn Khalaf . Daga Bangaren rundunar Musulmai kuma , babban kwamandansu shine SAYYIDUNA MUHAMMADUR RASULULLAHI (SAWW). Amma a karkashinsa akwai Manyan Kwamandodi kamar su: - Zakin Allah da Manzonsa ( Hamzatu bn Abdil Muttalib ). - Aliyyu Bn Abi Talib ( ra ). - Zubair bn Al- awwam (ra). -  Umar bn A...