Posts

Showing posts from November, 2023

KAMBUN IDO (MAITA) DA HANYOYIN MAGANCETA (01)

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM. Salati da aminci su tabbata bisa Annabin da aka bama Saba'ul Mathaniy da kuma Alqur'ani mai girma, Shugaban Masu fararen gabbai aranar Alqiyamah. Tare da iyalan gidansa inuwar al'ummah, da Sahabbansa yardaddu. Mun dade muna magana akan matsalar da ta shafi Massul Jinn (shafar Aljanu), Sihiri, da kuma Al-Ainu (kambun ido) ko Maita. Shi yasa yau na kuduri aniyar zan kawo mana wasu hanyoyi guda biyu ko uku wadanda za'a iya bi domin magance matsalar. Ita dai matsalar Kambun ido gaske ce ba Qarya ba. Domin Manzon Allah (saww) yayi bayaninta Qarara acikin hadisai da dama. Har ma yace "BAYAN QADDARAR ALLAH MADAUKAKIN SARKI, BABU ABINDA YAFI HALLAKAR DA AL'UMMATA FIYE DA KAMBUN IDO". Kuma yace "DA ACHE AKWAI ABINDA KE RIGA QADDARA AFKAWA KAN MUTUM, TO DA KAMBUN IDO YA RIGATA". Mafiya yawan masu Kambun ido, basu san ma suna dashi ba. Wadanda kuma suka san cewa suna da abun, basu cika bin hanyoyin da zasu kiyaye kansu daga chut