HADISINMU NA YAU
10th RAM ADHAN 1436 Hadisin zai yi magana ne akan KYAUTATA HALAYE. Kuma an karboshi ne daga Sayyiduna Jundub bn Junadah Wanda aka fi sani da ABU DHARRIN ALGHIFFARIY (RA) shi kuma ya karbo daga Manzon Allah (saww) yana cewa: "KAJI TSORON ALLAH A DUK INDA KAKE, KUMA KABI BAYAN MUMMUNAN AIKI DA KYAKKYAWA, ZATA SHAFETA. KUMA KAYI MA MUTANE MU'AMALA DA KYAKKYAWAN HALI". - Imam Tirmiziy ne ya ruwaito hadisin mai kyau ne. a wani wajen kuma yace hadisin mai kyawu ne kuma ingantacce ne. DARASI ********* Hakika wannan hadisin yana daga cikin Hadisan Manzon Allah (saww) wadanda suke da kalmomi Qalilan amma sun tattaro ma'anoni masu yawa. Hadisin yana kunshe ne da umurni guda uku kamar haka: 1. JIN TSORON ALLAH : Tsoron Allah acikin dukkan lamura, shine Tushen samun kowanne irin alkhairi na duniya da lahira. Ko acikin Alqur'ani Ubangiji ya gaya mana fa'idodin da masu tsoron Allah zasu samu. yace: - "KUJI TSORON ALLAH, ALLAH ZAI SANAR DAKU (ILIMI)".