HADISINMU NA YAU

10th RAMADHAN 1436

Hadisin zai yi magana ne akan KYAUTATA HALAYE. Kuma an karboshi ne daga Sayyiduna Jundub bn Junadah Wanda aka fi sani da ABU DHARRIN ALGHIFFARIY (RA) shi kuma ya karbo daga Manzon Allah (saww) yana cewa:

"KAJI TSORON ALLAH A DUK INDA KAKE, KUMA KABI  BAYAN MUMMUNAN AIKI DA KYAKKYAWA, ZATA SHAFETA. KUMA KAYI MA MUTANE MU'AMALA DA KYAKKYAWAN HALI".

- Imam Tirmiziy ne ya ruwaito hadisin mai kyau ne. a wani wajen kuma yace hadisin mai kyawu ne kuma ingantacce ne.

DARASI
*********
Hakika wannan hadisin yana daga cikin Hadisan Manzon Allah (saww) wadanda suke da kalmomi Qalilan amma sun tattaro ma'anoni masu yawa.

Hadisin yana kunshe ne da umurni guda uku kamar haka:

1. JIN TSORON ALLAH : Tsoron Allah acikin dukkan lamura, shine Tushen samun kowanne irin alkhairi na duniya da lahira.

Ko acikin Alqur'ani Ubangiji ya gaya mana fa'idodin da masu tsoron Allah zasu samu. yace:

- "KUJI TSORON ALLAH, ALLAH ZAI SANAR DAKU (ILIMI)".

- "DUK WANDA YAJI TSORON ALLAH, TO (ALLAH DIN) ZAI SANYA MASA MAFITA, KUMA ZAI AZURTASHI TA INDA BA YA TSAMMANI".

- "DUK WANDA YAJI TSORON ALLAH, TO (ALLAH DIN) ZAI KANKARE MASA LAIFUKANSA, KUMA ZAI GIRMAMA LADANSA GARESHI".

- "ALLAH YANA TARE DA MASU TSORON ALLAH".

- "MASU TSORON ALLAH SUNA DA ALJANNATAI NA NI'IMAH AWAJEN UBANGIJINSU".

- "WANDA YAJI TSORON TSAYAWA GA UBANGIJINSA YANA DA ALJANNONI GUDA BIYU".

Wannan jadan kenan daga fa'idodin da masu TSORON ALLAH zasu samu anan duniya da kuma Alqiyamah. Lallai tsoron Allah babu wani hali sama dashi.

2. YIN KYAWAWAN AYYUKA : Bayan Imani da Allah, ana so mutum kuma ya horar da gabobin jikinsa bisa kyautata ayyuka.

Idan TSORON ALLAH ya zauna azuciya, sannan gabobi suka aikata ayyukan alkhairi, to tabbas mutum zai rabauta da samun yardar Allah.

3. KYAUTATA HALAYE : Shima wannan babban jigo ne wanda duk wanda yayi riko dashi zai zauna lafiya tsakaninsa da Allah, da kuma tsakaninsa da bayin Allah. Kuma Manzo (saww) yace babu abinda yafi kyawun hali nauyaya mizanin Mutum aranar Alqiyamah.

An bama ANNABI (saww) labarin wata mata wacce take kwana sallah, sannan ta wuni da azumi. amma batta zama lafiya da makobtanta. Sai Manzon Allah (saww) yace : "ITA CE FARKON WACCE ZATA SHIGA WUTA".

ZAUREN FIQHU yana kira da babbar murya ga duk wanda ya karanta wannan rubutun yayi kokari ya fara aiki da darussan dake cikinsa domin samun dacewa awannan lokaci mai albarka.

SALLU ALAN NABIYYI (SAWW).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI