Posts

Showing posts from August, 2015

ANNABINA RAYAYYE NE ACIKIN QABARINSA

Wadansu mutane sun dauka cewar Manzon Allah (saww) ya riga ya rasu, ya tafi kenan, babu sauran wani hakkinsa akan su. Shi yasa basu damu da Girmamashi ko yawaita salati agareshi ba.. Malam Mai ZAUREN FIQHU ko zaka iya banu Hujjoji gamsassu akan cewa Ma'aiki (saww) yana nan raye acikin Qabarinsa? AMSA ******* Ba haka abin yake ba. Domin kuwa Manzon Allah (saww) yana ji, yana gani, har ma yana ibada acikin Qabarinsa. Kamar yadda Hujjoji zasu bayyana mana akan gaba. 1. Acikin Alqur'ani mai girma Allah ya gaya mana cewa Shaidai (wadanda suka mutu awajen Jihadi) ba mutuwa sukayi ba. suna nan rayayyu acikin Qabarinsu. Alkah yace: "KAR KUYI ZATON CEWA WADANNAN DA AKA KASHESU BISA TAFARKIN ALLAH, SU MATATTU NE. A'A SU RAYAYYU NE ANA CIYAR DASU AWAJEN UBANGIJINSU". Alqadhy Shawkaniy yace: "Acikin Alqur'ani ance mana Shaheedai rayayyu nd har ma ana ciyar dssu awajen Ubangijinsu. to gashi kuma Annabawa da Salihai suna sama dasu awajen daraja. To su yaya matsa