ANNABINA RAYAYYE NE ACIKIN QABARINSA
Wadansu mutane sun dauka cewar Manzon Allah (saww) ya riga ya rasu, ya tafi kenan, babu sauran wani hakkinsa akan su. Shi yasa basu damu da Girmamashi ko yawaita salati agareshi ba..
Malam Mai ZAUREN FIQHU ko zaka iya banu Hujjoji gamsassu akan cewa Ma'aiki (saww) yana nan raye acikin Qabarinsa?
AMSA
*******
Ba haka abin yake ba. Domin kuwa Manzon Allah (saww) yana ji, yana gani, har ma yana ibada acikin Qabarinsa. Kamar yadda Hujjoji zasu bayyana mana akan gaba.
1. Acikin Alqur'ani mai girma Allah ya gaya mana cewa Shaidai (wadanda suka mutu awajen Jihadi) ba mutuwa sukayi ba. suna nan rayayyu acikin Qabarinsu.
Alkah yace: "KAR KUYI ZATON CEWA WADANNAN DA AKA KASHESU BISA TAFARKIN ALLAH, SU MATATTU NE. A'A SU RAYAYYU NE ANA CIYAR DASU AWAJEN UBANGIJINSU".
Alqadhy Shawkaniy yace: "Acikin Alqur'ani ance mana Shaheedai rayayyu nd har ma ana ciyar dssu awajen Ubangijinsu. to gashi kuma Annabawa da Salihai suna sama dasu awajen daraja. To su yaya matsayinsu kenan?
Ingantattun Hadisai sun tabbatar mana da cewar su ma Annabawan suna nan araye acikin Qabarinsu. kumaImam Tirmizy da Baihaqiy sun ce hadisan ingantattu ne.
(Aduba NAYLUL AWTAAR na Shawkaniy din. Juzu'i na uku, shafi na 82.
2. HUJJAH TA BIYU: Hadisi daga Anas bn Malik (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"NA WUCE TA KUSA DA ANNABI MUSA ACIKIN DAREN DA AKAYI ISRA'I DANI, A KUSA DA WANI JAN TUDU, YANA TSAYE YANA SALLAH ACIKIN QABARINSA".
(aduba Sahihu Muslim hadisi na 5,858. da kuma Sunanun Nisa'iy hadisi na 1630 zuwa na 1636).
Afili Manzon Allah (saww) ya ganshi ba wai a mafarki ba. Kuma indai har Annabi Musa (as) yana nan raye har yana ibadah cikin Qabarinsa, to yaya kuma Jagoran dukkan Annabawa da Manzanni Maulana Muhammadur Rasulullahi (saww)??
3. HUJJAH TA UKU: wanu hadisin shima daga Anas bn Malik (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"ANNABAWA RAYAYYU NE ACIKIN QABURBURANSU. SUNA SALLAH".
(Aduba Hayatul Anbiya'i na Imamul Baihaqiy shafi na 03, MUSNADU ABIY YA'ALA juzu'i na 6, hadisi na 3425.
4. HUJJAH TA HUDU: Abu Hurairah (ra) ya ruwaito daga Manzon Allah (saww) yana cewa: "BABU WANI WANDA ZAI YI SALLAMA AGARENI FACHE SAI ALLAH YA MAYAR MIN DA RUHINA NA MAYAR MASA SALLAMAR".
- Abu Dawud ne ya ruwaito hadisin da Ingantaccen Isnadi.
- Suyutiy ya kawoshi acikin ALHAWIY LIL FATAWIY juzu'i na 2, shafi na 271 zuwa na 272.
- Shaukaniy ma ya inganta hadisin acikin NAYLUL AWTAAR juzu'i na 5, shafi na 164.
*************
DAGA ZAUREN FIQHU : Wannan ayar da kuma hadisan hujjah ne akan cewa Annabawa rayayyu ne acikin Qabarinsu. Kuma suna ji suna magana, har ma suna Ibadah.
Kuma duk inda kake, babu laifi ka halarto Manzon Allah (saww) azuciyarka, kayi masa salati sannan ka gaisheshi da tasleemi kamar kace "ASSALAMU ALAIKA AYYUHAN NABIYYU WA RAHMATULLAH WA BARAKATUH". Ballantana kuma idan kaje Ziyararsa (saww).
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (BB PIN (5644D76B)
S.A.W
ReplyDelete