Posts

Showing posts from October, 2015

HAKKOKIN IYALAN GIDAN ANNABI (SAWW)

HAKKOKIN IYALAN GIDAN ANNABI (SAWW). ********************************************** Da sunan Allah buwayi Gagara-Misali. Wanda yake zabar wanda yaso ya fifitashi da falalarsa, ya kebanceshi da fifikonsa. Dukkan Tsira da aminci da yarda da albarkoki da ni'imomi da rahama su tabbata ga Mabudin dukkan alkhairai, Shugaban Mutanen farko da na karshe, kuma Makullin Zurin Annabta da Manzanci, Masoyinmu, Abincin zukatanmu, Annabi Muhammadu, Tare da iyalan gidansa tsarkaka masu albarka, da dukkan Sahabbansa Shiryayyu. Mun shirya wadannan lakchochi ne daga ZAUREN FIQHU WHATSAPP domin warware wasu muhimman batutuwan da suka shafi Iyalan gidan Manzon Allah (saww) tare da yin bayani akansu da falalarsu da kuma hakkokinsu wadanda suka rataya bisa wuyan dukkan Muminai. Sannan in sha Allahu zamu kawo misalai na irin Zurfafawar da wasu suke yi da sunan wai suna son Ahlul baiti (amma basu bin tafarkinsu). Allah ya san ina Qaunar Ahlul Baiti fiye da yadda nake son kaina da iyayena.. Amma ba kom