HAKKOKIN IYALAN GIDAN ANNABI (SAWW)

HAKKOKIN IYALAN GIDAN ANNABI (SAWW).
**********************************************
Da sunan Allah buwayi Gagara-Misali. Wanda yake zabar wanda yaso ya fifitashi da falalarsa, ya kebanceshi da fifikonsa.

Dukkan Tsira da aminci da yarda da albarkoki da ni'imomi da rahama su tabbata ga Mabudin dukkan alkhairai, Shugaban Mutanen farko da na karshe, kuma Makullin Zurin Annabta da Manzanci, Masoyinmu, Abincin zukatanmu, Annabi Muhammadu, Tare da iyalan gidansa tsarkaka masu albarka, da dukkan Sahabbansa Shiryayyu.

Mun shirya wadannan lakchochi ne daga ZAUREN FIQHU WHATSAPP domin warware wasu muhimman batutuwan da suka shafi Iyalan gidan Manzon Allah (saww) tare da yin bayani akansu da falalarsu da kuma hakkokinsu wadanda suka rataya bisa wuyan dukkan Muminai.

Sannan in sha Allahu zamu kawo misalai na irin Zurfafawar da wasu suke yi da sunan wai suna son Ahlul baiti (amma basu bin tafarkinsu).

Allah ya san ina Qaunar Ahlul Baiti fiye da yadda nake son kaina da iyayena.. Amma ba komai ne yasa na fara wannan rubutun ayanzu ba, sai ganin yadda mutane suka jahilci Lamarin Ahlul Baiti.

Wadansu sun daukesu amatsayin abin Kyama, abin wulakantarwa, abin nesantarwa. Wadansu kuma sun daukesu kamar alloli ababen bauta. Wadansu kuma basu sansu ba ma kwata-kwata.

Har an kai matsayin yadda Manyan Malamai ma suna jin tsoron fitowa su fadi falalar Ahlul baiti don tsoron kar a chanza musu suna..

Kafin inci gaba da wannan rubutun zanso masu karatu su dubi dukkan abinda zan rubuta da idon basira, ba da idanu na zargi ba.

Ku sani cewa duk abinda zan kawo sai na fadi littafin da na ciroshi. Babu Qirkira ko Qage. Duk abinda zamu rubuta zai zama tare da hujjah ne.

Kuma ku sani cewa bani da wata alaqah da shi'a ko Malamansu ko litattafansu. Kuma idan kun fahimci duk abinda zai zo nan gaba acikin lakchochin da zasu biyo baya, zaku gane cewa babu ruwan Ahlul Baiti da irin abinda Shi'a suke yi.

SHIN SU WAYE AHLUL BAITI?
*******************************
Akwai sabani mai yawa tsakanin bangarorin malamai dangane da wannan mas'alar.

Kwanakin baya acikin wata munazarah na kawo ra'ayoyin Malaman Fiqhu da dama akan haka. Yanzu ma zan maimaita in sha Allahu saboda cikar fa'idah.

Hakika malamai sunyi sabani akan abinda ake nufi da ahlul baiti. Fahimtar Malaman ta kasu zuwa gida uku kamar haka.

KASO NA FARKO: Imam Shafi'iy da Ahmad (a wani Kaulin) sunce Ahlul baiti sune Banu Hashim baki dayansu tare da Banul Muttalib.

Awani Qaulin kuma Imam Abu Hanifah yace Banu Hashim su kadai sune ahlul bait. Hakanan Imamu Ahmad da Ibnul Qasim (almajirin Imamu Malik) su ma haka suka ce.

Malam Ash-Habu kuma (daga Mazhabin Malikiyyah) yace Ahlul Baiti sun fara ne tun daga kan Ghalibu (kakan Manzon Allah saww) da dukkan Zuriyarsa.

KASO NA BIYU : Sune malaman da suka ce Ahlul baitu sune Matan Manzon Allah (saww) da zuriyyarsa kadai.  (kamar yadda Ibnu Abdil-Barri ya kawo acikin Littafinsa AT-TAMHEED).

KASO NA UKU : Sune malaman da suka ce ai Ahlul baiti ana nufin dukkan Mabiyan Manzon Allah (saww) ne har ya zuwa tashin alkiyamah.

Amma Ibnul Qayyim ya raunana wannan ra'ayin na uku acikin littafinsa JILA'UL AF-HAAM inda ya kawo ra'ayin kowanne bangare tars da dalilansu masu karfi ko rauni daidai gwargwado.

Malam Zujaaj (rah) yace Wadanda ake nufi da iyalan gidan Manzon Allah (saww) sune :

1. Matayensa baki dayansu.

2. Zuriyarsa: Wato Nana Fatima, Sayyiduna Aliyu, Imam Hasan, da kuma Imamul Husaini (Allah shi Qara yarda dasu).

Akwai kuma Malaman da suke ganin cewa Ahlul Baiti sune :

1. Matayen gidan Annabi (saww).

2. Iyalan gidan Baffansa Abbas (ra).

3. Iyalan gidan Sayyiduna Aliy.

4. Iyalan gidan Aqeel bn Abi Talib (ra).

5. Iyalan gidan Ja'afar bn Abi Talib (ra).
Allah shi Qara musu yarda baki daya.

Abinda yake Qara ma wannan Qaulin Qarfi shine cewa wadannan iyalan gidan da na lissafa sune wadanda aka haramta musu cin sadaqah. Saboda Qaulin Manzon Allah (saww) :

"HAKIKA ITA WANNAN SADAQAH DIN ITA BA KOMAI BANE SAI DAI TANA DAGA CIKIN DAU'DAR MUTANE NE. DON HAKA BATA HALATTA GA MUHAMMADU BA, BALLANTANA GA IYALAN GIDANSA".

(Imamu Muslim ne ya fitar da hadisin acikin Kitabuz Zakat).

Shi kuwa wancan Qaulin na Imam Zujaaj shima akwai hujjar da take karfafarsa kamar haka : Hadisin da Tirmizy ya ruwaito daga Sayyidah Ummu Salamah (ra) cewa:

"Fatimah da Hasan da Husayni da Mahaifinsu (Imam Aliyu) sun taru adakinta sai Manzon Allah (saww) ya lullubesu da mayafinsa sannan yace :

"YA ALLAH WADANNAN SUNE IYALAN GIDANA. (INA ROKONKA) KA TAFIYAR DA DAU'DA DAGA GARESU, KUMA KA TSARKAKESU MUTUKAR TSARKAKEWA".

Sai Ita Sayyidah Ummu Salamah tace "Nima ina tare dasu Ya Rasulallahi?".

Sai yace : "Ki zauna a inda kike, kuma kema kina bisa alkhairi".

Malamai sunyi sa'bani akan dalilin da yasa Manzon Allah (saww) bai ce mata ta shigo ba.

1. Wasu suka ce yace mata kar ta shigo ne, wato ba sai kin shigo ba. Ai tuntuni kema kina cikin iyalan gidana. Don haka baki da bukatar shigowa cikin bargon nan. Wato ya hanata ne saboda daukakar matsayinta.

2. Wasu kuma suka ce ma'anarsa,  Kema kina bisa alkhairi koda dai baki cikin iyalan gidana.

Amma wancan maganar ta farko ita ce tafi rinjaye, kuma ita ce Sahihiya. Kuma ita ce ainihin abinda Manzon Allah (saww) yake nufi.

Daga cikin hujjojin da suke karfafar hakan akwai hadisin da Ibnu Katheer ya kawo acikin tafseerinsa ta hanyar Ibnu Jareer At-Tabariy daga Abdullahi bn Wahab yace Ummu Salamah ta bani labari cewa:

"Manzon Allah (saww) ya tattaro Aliyu da Fatima da Hasan da Husaini sannan ya shigar dasu Qasan tufafinsa. Sannan yayi roko ga Allah Madaukakin sarki yana cewa "WADANNAN SUNE IYALAN GIDANA"

Aai nace masa "Ya Rasulallahi nima ka shigar dani cikinsu".

Sai yace min "AI KEMA KINA CIKIN IYALAN GIDANA".

Duk mai bukatar Qarin bayani akan wannan yaje ya duba Maraji'u kamar haka:

1. TUHFATUL AHWAZEE (Sharhin Tirmidhy) juzu'i na 9, shafi na 66-67.

2. TAFSEER na Ibnu Katheer juzu'i na 6, shafi na 246-247.

3. AS-SAWAA'IQUL MUHRIQAH (Na Haithamiy) juzu'i na biyu shafi na 656.

Anan zamu tsaya sai a karatu na gaba, zamu dora da yardar Allah.

An gabatar da karatun ne a ZAUREN FIQHU WHATSAPP (1) Lahadi 12 ga Almuharram 1437.

Tsira da amincin Allah su tabbata bisa Annabin Mutane da Aljanu, Shugabanmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (1).

Comments

  1. Hi ! here you can download Shugaban Mutane Da Aljannu in Hausa, a most authentic and renowned Islamic Book.
    http://www.dislamicbooks.com/2015/12/download-shugaban-mutane-da-aljannu-pdf.html
    The book is also available in English, Urdu and other Languages.

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI