DUNIYAR ALJANU DA ABINDA TA QUNSA (003)
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP B ISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM Salati da amincin Allah su tabbata ga Annabin da aka aikoshi zuwa ga dukkan Halittu baki daya, Shugabanmu Muhammad tare da iyalan gidansa Masu albarka da Sahabbansa yardaddu. Idan daliban Wannan Zauren basu manta ba, acikin wancan karatun namu mun warware wasu mas'aloli dangane da sha'anin duniyar aljanu. Munyi bayani akan wuraren zamansu da kamanninsu da kuma abincinsu kamar yadda Ayoyin Alqur'ani Mai Girma da kuma Sahihan hadisai suka tabbatar. Yanzu kuma zamu dora daga inda muka tsaya in sha Allahu. S H AITAN YANA DA QAHO *************************** Tabbas lallai shaitan yana da Qaho akansa. Kamar yadda wasu da dama daga cikin Shaitanun Aljanu su ma suna dashi. Akwai hadisi wanda yake tabbatar da hakan. An ruwaitoshi daga Sayyiduna 'Amru bn 'Anbusata (rta) yace Manzon Allah (saww) yace : " HA KIKA ITA RANA TANA FITOWA NE TA TSAKANIN QAHOHUNA BIYU NA WANI SHAITANI, KUMA TANA FA'DUWA NE