DUNIYAR ALJANU DA ABINDA TA QUNSA (003)

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

Salati da amincin Allah su tabbata ga Annabin da aka aikoshi zuwa ga dukkan Halittu baki daya, Shugabanmu Muhammad tare da iyalan gidansa Masu albarka da Sahabbansa yardaddu.

Idan daliban Wannan Zauren basu manta ba, acikin wancan karatun namu mun warware wasu mas'aloli dangane da sha'anin duniyar aljanu.

Munyi bayani akan wuraren zamansu da kamanninsu da kuma abincinsu kamar yadda Ayoyin Alqur'ani Mai Girma da kuma Sahihan hadisai suka tabbatar.

Yanzu kuma zamu dora daga inda muka tsaya in sha Allahu.

SHAITAN YANA DA QAHO
***************************
Tabbas lallai shaitan yana da Qaho akansa. Kamar yadda wasu da dama daga cikin Shaitanun Aljanu su ma suna dashi.

Akwai hadisi wanda yake tabbatar da hakan. An ruwaitoshi daga Sayyiduna 'Amru bn 'Anbusata (rta) yace Manzon Allah (saww) yace :

"HAKIKA ITA RANA TANA FITOWA NE TA TSAKANIN QAHOHUNA BIYU NA WANI SHAITANI, KUMA TANA FA'DUWA NE TA TSAKANIB QAHOHUNA BIYU NA WANI SHAITANIN".

Hadisi ne Sahihi. Imamul Bukhariy ya kawoshi akan lambar hadisi na 3,273 acikin babin dake magana akan Siffofin Iblees.

Imamu Muslim kuma ya kawoshi akan lambar hadisi na 828.

SHIN DA GASKE NE ALJANU SUNA IYA RIKIDEWA (CHANZA KAMANNINSU)??

Eh da gaske ne tabbas Aljanu da Shaitanu sukan chanza Kamanninsu zuwa duk wata siffar da suka ga dama.

Tun azamanin Manzon Allah (saww) da sahabbansa an samu Misalai da dama akan haka.

Misali kamar lokacin da Manzon Allah (saww) ya sanya Abu Hurairah gadin abincin Zakkah, sai wani Shaitani ya rikide yazo a Siffar mutum yana satar abincin.

Sau Uku ajere Abu Hurairah (ra) yana kamashi akan zai kaishi wajen Manzon Allah (saww) shi kuma yana yi masa magiyar cewa ba zai dawo ba.

A karo na uku ne yace masa idan ya kyaleshi zai sanar dashi abinda zai amfaneshi. Shine yace masa ya rika karanta ayatul kursiyyi duk sanda zai kwanta barcinsa.

Abu Hurairah yazo ya gaya ma Manzon Allah (saww) sai yace masa "SHIN KO KASAN DA WANDA KAKE MAGANA ACIKIN DARARE UKUN NAN KUWA?"

Yace masa "A'a". Sai yace masa "AI SHAITANI NE".

Hadisin yana nan acikin Sahihul Bukhariy lamba ta 2,311.

Sannan akwai hadisi acikin Sunanun Nisa'iy daga Sayyiduna Ubayyu bn Ka'ab (ra) cewa yana da wani wajen da yake shanyar dabino sai ya kasance duk lokacin da yazo ya duba sai yaga dabinon nasa yana raguwa. Don haka ya fara fako ko zai ga mai satar masa dabinon.

Yace nazo rannan na leka kawai sai naga wata dabba mai kamar Yaro saurayi.

Sai nace masa "Kai Aljani ne ko Mutum ne?" Sai yace mun "A'a Ni Aljani ne".

Sai nace masa "To matso kusa in ganka".

Da ya matso kusa sai ba rike hannayensa, sai naji su Kamar Qafafun kare.

Sai nace masa "Shin Haka Halittar Aljanu take?" Sai yace "Kwarai kuwa. Kuma su kansu Aljanu sun san cewar ina daga cikin Mafiya Qarfun Jiki acikinsu".

Yace "Ai mun samu labarin cewar Kai mutum ne mai son yin Sadaqah shi yasa muke son Muci irin abincinka".

Sai nace masa "Shin wanne abu ne zai Karemu daga gareku?" Sai yace "Wannan AYATUL KURSIYYI din nan".

Da Ubayyu din yazo ya gaya Manzon Allah (saww) labarin yadda sukayi sai yace masa "QAZAMIN NAN YAYI GASKIYA".

Al-Hafiz Ibnu Hajr Al-Asqalaniy (rah) ya kafa Hujjah da wadannan hadisan guda biyu cewa Shaitan ma yakan iya surantuwa ya chanza siffah zuwa ga wasu kamanni wadanda zai yiwu Mutane su iya ganinsa.

Hafiz yace ayar nan wacce Allah yake cewa : "HAKIKA SHI DA QABILARSA SUNA GANINKU NE TA YADDA KU BAKU GANINSU".

Yace wannan ayar ta kebantu ne da lokacin da Shi Shaitan din ko Aljanun suke cikin ainahin siffarsu wacce Allah ya haliccesu akanta. Amma idan suka rikide, zai yiwu arika ganinsu da siffofi mabambanta.

Don Qarin bayani aduba cikin FAT'HUL BAARIY juzu'i na 4, shafi na 489.

Kuma akwai Sahihan hadisai wadanda suka nuna cewar Aljanu sukan rikida zuwa Siffar Karnuka ko Macizai. Musamman Bakaken Karnuka.

Su kuwa Macizai, ashe ainahinsu ma Aljanu ne. An juyar da siffarsu ne zuwa haka saboda wasu dalilai. Kamar yadda Annabi (saww) yace :

"MACIZAI AN RIKIDAR DASU NE DAGA ALJANU (WATO AINAHINSU ALJANU NE) KAMAR YADDA AKA RIKIDAR DA BIRRAI DA ALADAI (MONKEYS AND PIGS)  DAGA AL'UMMAR BANU ISRA'IL (WATO YAHUDAWA)".

Hadisi ne Sahihi aduba Sahihu Ibni Hibbaan, hadisi na 1,080.

MU'UJAMUL KABEER na Tabaraniy hadisi na 11,946.

AL-ILAL na Ibnu Abee Hatam juzu'i na 2, shafi na 290.

Acikin wani Sahihin hadisin kuma yace "DA BA DON KARNUKA MA AL'UMMAH GUDA BANE, DA NAYI UMURNI ARIKA KARKASHESU.

SAI DAI INA TSORON KAR IN QARAR DA WATA AL'UMMAH NE.

AMMA KU KASHE DUK WANI BAQIN (KARE) MAI JA-JAN IDANU, DOMIN SHI WANNAN YANA DAGA ALJANUN CIKINSU NE".

Sahihu Muslim hadisi na 1572.

Hakanan acikin Sahihu Muslim din akwai wani hadisin wanda acikinsa Manzon Allah (saww) ya lissafa wasu abubuwa guda uku wadanda idan sun wuce ta gaban Mai Sallah (in dai bai sanya Sutrah ba) zasu iya 'bata masa sallarsa. Sune kamar haka :

* Jaki
*  Mace.
* Baqin Kare.

Akarshen hadisin Manzon Allah (saww) yace : "BAQIN KARE SHAITANI NE".

Aduba Sahihu Muslim hadisi na 510.

Sunanun Nisa'iy juzu'i na 2 shafi na 64.

Ibnu Maajah juzu'i na 1, shafi na 306.

Sunanud Darimiy juzu'i na 1, shafi na 329.

Lallai wadannan hadisan sun Qara fito da abun afili cewar Aljanu da Shaitanu sukan rikida. Har ma su fito a siffar Mutum ko Dabba.

Kuma ga hujjoji nan bayyanannu wadanda duk mai hankali zai iya dogaro dasu akan haka.

An zamu tsaya sai a karatu na gaba kuma in sha Allahu zamu dora daga kan .

An gabatar da karatun ne a ZAUREN FIQHU WHATSAPP 3 da 4 ranar Talata 1 ga December 2015.

Tsira da aminci su tabbata ga Annabin Farko da Qarshe tare da iyalan gidansa masu albarka da Sahabbansa.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI