BANKUNAN AJIYAR RUWAN MANIYYI
Yanzun nan ina zaune sai naga shigowar wata wasika daga wani 'Dan uwa kuma member a Zauren Fiqhu Whatsapp -1. Yana jan hankalina zuwa ga karanta wani bayani da ya kwafo ya turo mun. (Daga shafin wata Jaridar Qasar nan).
Wato bayanin yana kunshe ne da wani Quduri wanda wata Cibiyar binciken yanayin rayuwa da kuma tattalin arzikin Nigeria (NISER) dake Ibadan ta gabatar.
Cibiyar tayi kira ne ga Gwamnatin Tarayyar Nigeria cewar ta kafa "SPERM BANKS" (Rumbunan ajiyar ruwan Maniyyi da Qoyayyen Halitta) a sasannin Nigeria.
Cibiyar ta gabatar da wannan kiran ne acikin wata takarda wacce daya daga cikin Wakilanta DR THERESA ORIAKU EMORDI ta Jami'ar Obafemi Awolowa ta gabatar awajen wata Seminar.
Sun bukaci ma asanya Qudurin ya zama doka a Qasar nan cewa Matsalar rashin haihuwa dole sai an magance matsalar rashin haihuwa atsakanin Ma'aurata.
Shi dai wannan bankin ajiyar Maniyyi idan har an Qirkireshi, to zai bada damar kowanne mutum zai iya zuwa