BANKUNAN AJIYAR RUWAN MANIYYI

Yanzun nan ina zaune sai naga shigowar wata wasika daga wani 'Dan uwa kuma member a Zauren Fiqhu Whatsapp -1. Yana jan hankalina zuwa ga karanta wani bayani da ya kwafo ya turo mun. (Daga shafin wata Jaridar Qasar nan).

Wato bayanin yana kunshe ne da wani Quduri wanda wata Cibiyar binciken yanayin rayuwa da kuma tattalin arzikin Nigeria (NISER) dake Ibadan ta gabatar.

Cibiyar tayi kira ne ga Gwamnatin Tarayyar Nigeria cewar ta kafa "SPERM BANKS" (Rumbunan ajiyar ruwan Maniyyi da Qoyayyen Halitta) a sasannin Nigeria.

Cibiyar ta gabatar da wannan kiran ne acikin wata takarda wacce daya daga cikin Wakilanta DR THERESA ORIAKU EMORDI ta Jami'ar Obafemi Awolowa ta gabatar awajen wata Seminar.

Sun bukaci ma asanya Qudurin ya zama doka a Qasar nan cewa Matsalar rashin haihuwa dole sai an magance matsalar rashin haihuwa atsakanin Ma'aurata.

Shi dai wannan bankin ajiyar Maniyyi idan har an Qirkireshi, to zai bada damar kowanne mutum zai iya zuwa ya bada kyautar Maniyyinsa, sannan kowacce Mata ma zata iya zuwa ta karba daga hannun Hukuma domin aje asanya mata shi wannan Maniyyin acikin mahaifarta domin neman haihuwa.

To babban kiran da Zauren Fiqhu zai yi zuwa ga Shugabannin Hukumomin Nigeria shine, duk da cewar Qasar nan tamu akwai mabiya addinai dabam dabam, to amma Musulmai sunfi rinjaye. Don haka duk abinda Gwamnati zata zartar ya kamata ta rika tuntubar Maluma domin tabbatar daa cewa bai sa'ba ma dokokin addininmu ba.

Mu a Musulunci dole ne kiyaye nasabar 'Dan Adam. Don haka bai halatta ga wani Musulmi yaje ya bayar da Maniyyinsa don ajiyewa a irin wadannan guraren, ko kuma don amfanar da wani ko wata ba. Sai dai Matarsa ta aure.

Hakanan bai halatta a dauki Maniyyin wani mutum a sanya acikin mahaifar wata Mace ba. Sai dai in Mijinta ne shi.

Sannan bai halatta ga wata Mace ta dauki Kwan halittarta ta bayar domin amfani ga wani ko wata ba.

Su Turawa da Yahudawa sun dade suna yin wannan "SPERM DONATIONS" din a kasashensu. Har ma daga nan Africa akwai masu hannu da shuni wadanda sukan je ayi musu. Wato asanya ma Matarsu ruwan Maniyyin wani Namijin acikin Mahaifarta (Don sun riga sun haukace akan son haihuwa).

Muna kira ga hukumomi cewa suyi watsi da irin wadannan kiraye-kirayen. Kuma muna kira ga dukkan Musulmai cewar su guji aikata irin wannan domin ya sa'ba ma dokokin addinin Musulunci.

Allah yasa wadanda akayi dominsu su gani su kiyaye.

DAGA ZAUREN FIQHU 28-10-2016 (26-01-1438) Mai bukatar Qarin bayani ko fatawa akan wannan Mas'alar zai iya kiran lambar Zauren Fiqhu (07064213990)

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI