Posts

Showing posts from January, 2019

DARAJOJIN AHLUL BAITI (ALAIHIMUS SALAM)

MU SAN ANNABINMU (16)

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, Salati da amincinsa su tabbata ga Zababben Zababbunsa Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa da Sahabbansa baki daya Wannan ita ce fitowa ta goma sha shida acikin darasin Zauren Fiqhu wanda ke kawo muku tarihin Shugaban Halitta (saww) kuma in shaAllah zamu dora daga inda muka tsaya. HIJIRAR FARKO ZUWA HABASHA : Yayin da cutarwar Mushrikai ta Qara tsananta ga duk jama'ar da suka shiga addinin Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam), sai ya umurcesu da yin hijira zuwa Qasar habasha (wato yankin Qasar Ethiopia ta yanzu, anan nahiyar Africa) domin su tseratar da addininsu, Kuma ya basu labarin cewa achan Habasha din akwai wani sarki wanda ke mulkarsu, sunansa Najjashi kuma ba ya yarda a zalunci kowa akarkashin mulkinsa. Adadin wadanda sukayi wannan hijira mutum goma sha shida ne. Wato mazaje goma sha daya ne tare da mataye biyar. Kuma sunyi wannan hijirar ne acikin shekara ta biyar bayan aika wato shekaru takwas kafin hijira kenan.