MU SAN ANNABINMU (16)
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, Salati da amincinsa su tabbata ga Zababben Zababbunsa Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa da Sahabbansa baki daya
Wannan ita ce fitowa ta goma sha shida acikin darasin Zauren Fiqhu wanda ke kawo muku tarihin Shugaban Halitta (saww) kuma in shaAllah zamu dora daga inda muka tsaya.
HIJIRAR FARKO ZUWA HABASHA :
Yayin da cutarwar Mushrikai ta Qara tsananta ga duk jama'ar da suka shiga addinin Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam), sai ya umurcesu da yin hijira zuwa Qasar habasha (wato yankin Qasar Ethiopia ta yanzu, anan nahiyar Africa) domin su tseratar da addininsu, Kuma ya basu labarin cewa achan Habasha din akwai wani sarki wanda ke mulkarsu, sunansa Najjashi kuma ba ya yarda a zalunci kowa akarkashin mulkinsa.
Adadin wadanda sukayi wannan hijira mutum goma sha shida ne. Wato mazaje goma sha daya ne tare da mataye biyar. Kuma sunyi wannan hijirar ne acikin shekara ta biyar bayan aika wato shekaru takwas kafin hijira kenan.
Basu fi shekara guda achan ba sai wani labari marar tushe ya iskesu cewa ai lamura sunyi kyau agarin Makkah, kuma mutane da yawa sun musulunta, har an dena chutar da Musulmai. Daga jin haka sai sukayi murna suka komo gida Makkah.
HIJIRA TA BIYU ZUWA HABASHA :
Amma bayan dawowarsu sai suka tarar da sa'banin abinda suke zato, wato yanayin ma har yafi tsanani fiye da wancan da suka sani. Don haka suka sake shirin komawa Qasar Habasha tare da Qarin wasu. Yanzu adadun nasu ya kai har mutum dari. Mazaje tamanin da biyu, mataye goma sha takwas.
Wannan ya faru ne acikin shekara ta shida bayan aike. Kuma dalili ne bisa irin tsananin chutarwar da suke riska a hannun kafiran Makkah.
Su kuwa kafiran Makkah da suka ga haka sai sukayi shiri suka aiki wani mai hikima daga cikinsu wato Amru 'dan Aasi ya bisu chan Qasar Habasha tare da kyaututtuka zuwa ga Sarkin da fadawansa ya nemi cewa akoro wadannan da sukayi hijira zuwa Qasar.
Yayin da Najjashi yaji abinda Amru dan Aasi (wakilin kafiran Makkah alokacin bai musulunta ba) ya nema daga gareshi, sai ya aika aka kirawo masu hijirar, su kuma suka wakilta Sayyiduna Ja'afar bn Abi Talib (radhiyallahu anhu) ya fito ya karesu daga abinda Quraishawan suka nema awajen Najjashi, kuma ya sanar dashi cewa su sun taho Qasarsa ne domin guje wa chutarwa da tsanantawar da ake yi musu saboda addininsu. Da Najjashi yaji haka sai ya kori wakilin kuraishawa (wato Amru dan Aasi) ya mayar masa da kyautukan da ya kawo kuma ya sanar dashi cewa ba zai biya ma Kuraishawa wannan mummunan bukatar tasu ba.
Anan zamu tsaya sai a karatu na gaba zamu dora daga inda muka tsaya.
An gabatar da karatun ne a ZAUREN FIQHU WHATSAPP 1 ranar Lahadi 21/05/1440 27/01/2019.
Comments
Post a Comment