Posts

Showing posts from January, 2020

TAMBARIN ANNABTARSA (SAWW)

TAMBARIN ANNABTARSA (SAWW) *********************************** Kowanne Annabi daga cikin Annabawan Allah (alaihimus salam) yana da tambarin Annabta ajikinsa. Dukkan Annabawa tambarinsu yana bisa tafin hannunsu ne, amma Annabinmu Muhammadu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) shi ka'dai ne wanda aka sanya masa nasa ta bayansa atsakanin kafadunsa, wato daidai saitin zuciyarsa mai tsarki (saww). Shaikh Hisham bn Alkamil ya fa'da acikin sharhin Shama'ilul Muhammadiyyah cewa "Lokacin da aka haifeshi khatimin Annabtar yana boye ne acikin jikinsa. Har sai da lokacin aikoshi yayi, sannan Mala'ika Jibreelu (alaihis salam) ya fito dashi daga cikin zuciyarsa sannan ya bugashi atsakanin kafadunsa. Hakanan bayan wafatinsa Sayyidah Asma'u bintu Umaisin ta sanya hannunta adaidai wajen da Khatimin yake, amma bata jishi ba. Daga jin haka ta fahimci cewa lallai Ubangijinsa ya karbeshi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Tirmidhiy Al Hakeem yace "Allah ya hali