TAMBARIN ANNABTARSA (SAWW)
TAMBARIN ANNABTARSA (SAWW)
***********************************
Kowanne Annabi daga cikin Annabawan Allah (alaihimus salam) yana da tambarin Annabta ajikinsa. Dukkan Annabawa tambarinsu yana bisa tafin hannunsu ne, amma Annabinmu Muhammadu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) shi ka'dai ne wanda aka sanya masa nasa ta bayansa atsakanin kafadunsa, wato daidai saitin zuciyarsa mai tsarki (saww).
Shaikh Hisham bn Alkamil ya fa'da acikin sharhin Shama'ilul Muhammadiyyah cewa "Lokacin da aka haifeshi khatimin Annabtar yana boye ne acikin jikinsa. Har sai da lokacin aikoshi yayi, sannan Mala'ika Jibreelu (alaihis salam) ya fito dashi daga cikin zuciyarsa sannan ya bugashi atsakanin kafadunsa.
Hakanan bayan wafatinsa Sayyidah Asma'u bintu Umaisin ta sanya hannunta adaidai wajen da Khatimin yake, amma bata jishi ba. Daga jin haka ta fahimci cewa lallai Ubangijinsa ya karbeshi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).
Tirmidhiy Al Hakeem yace "Allah ya halicci Khatimin ne da irin naman jikin Annabi (saww) wato tamkar tsirowa yayi ajikin nasa. Akwai gashi ka'dan ajikinsa, kuma akwai rubutu akansa an rubuta "Tawajjah haithu shi'ita fa'innaka mansurun". *(SA GABANKA DUK INDA KASO, DOMIN HAKIKA KAI ABIN TAIMAKO NE)*
Bukhariy da Muslim da Tabaraniy da Tirmidhiy sun ruwaito daga Al Ja'adu dan Abdurrahman yace "Naji Assa'ibu 'dan Yazeedu (Allah ya yarda dashi) yana cewa :
"'Yar uwar mahaifiyata ta tafi dani wajen Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) tace "Ya Ma'aikin Allah! Hakika 'dan 'yar uwata din nan yana fama da jinya".
Sai ya shafi kaina kuma ya roka mun albarka. Yayi alwala kuma nasha ruwan alwalar tasa, na tsaya ta wajen bayansa na kalli tambarin Annabta atsakanin kafadunsa kamar misalin Qwan tattabara yake".
Allahu Akbar!! Ya Allah yi salati da amincinka bisa Annabinmu Shugabanmu Muhammadu tare da iyalan gidansa da dukkan Sahabbansa da Salihan bayinka baki daya.
DAGA ZAURN FIQHU 07064213990 (29/07/2019 26/11/1440).
Comments
Post a Comment