Posts

Showing posts from January, 2021

HANNUNKA MAI SANDA (45)

Wani lokacin  idan nayi nazari game da yadda tarbiyyar matasa Maza da mata ta tabarbare awannan zamanin da muke ciki, bisa la'akari da abin dake faruwa a zahiri da kuma kan kafofin sadarwa, hankalina yakan Qara tashi  sosai idan nayi tunanin : TO YAYA AL'UMMAR DA ZASU ZO ABAYANMU ZASU KASANCE??  Yanzu mu a wautarmu ta 'yan zamani muna ganin kamar munfi iyayenmu da kakanninmu wayewa (watakil saboda yaduwar ilimi da kuma ci gaban da muke ganin an samu alokacin wanda babu shi anasu zamanin, to amma idan muka dubi lamarin ta fuskar  addini zamu ga cewa iyayenmu da kakaninmu: Sun fimu kirki.  Sun fimu tsoron Allah.  Sun fimu zumunci.  Sun fimu tsayawa kan gaskiya.  Sun fimu rikon amana.  Sun fimu kunya.  Sun fimu kula da sallah.  Sun fimu biyayyar aure.  Sun fimu kula da hakkin iyali.  Sun fimu biyayya ga nasu iyayen.  Sun fimu kula da hakkin makobta.  Sun fimu taimakon addini.  Sun fimu nisantar manyan zunubai.  Mu kuwa bamu fisu da komai ba, fache wayrear kai na Qarya, da bush