Posts

Showing posts from 2024

HALAYEN MASU TSORON ALLAH

HALAYEN MASU TSORON ALLAH (07). DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP  BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM. Salati da amincin Allah su tabbata bisa Shugaban masu tsoron Allah, Annabi Muhammadu mabudin dukkan alkhairi farin jakada.. Tare da iyalan gidansa masu alfarma da Sahabbansa masu albarka. Da dukkan wadanda suke biye da tafarkinsu har zuwa ranar tsaiwa. Idan ba'a manta ba, muna ci gaba da haskowa wasu abubuwa daga rayuwar magabatanmu ne musamman abinda ya shafi bangaren yanayin ibadarsu, da kuma yadda zukatansu suke narkewa cikin tsoron Allah da kuma tunanin lahirarsu. Daga cikinsu akwai Ibnu Wahbin watarana ya shiga bandaki sai yaji wani (daga waje) yana karanta ayar nan ta cikin Suratul Ghafir (Wa iz yatahaajjuuna Finnari). Acikin ayar Allah yana bayanin yadda 'yan wuta suke jayayya atsakanin junansu ne...  Shi kuwa daga jin wannan Qira'ar nan take ya Fa'di Qasa ya suma.. Har sai da aka wankeshi da ruwan sanyi bai farfado ba. Ita kuwa Mu'azatul Adawiyyah ('yar uwar Rabi'