HALAYEN MASU TSORON ALLAH

HALAYEN MASU TSORON ALLAH (07). DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP 

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

Salati da amincin Allah su tabbata bisa Shugaban masu tsoron Allah, Annabi Muhammadu mabudin dukkan alkhairi farin jakada.. Tare da iyalan gidansa masu alfarma da Sahabbansa masu albarka. Da dukkan wadanda suke biye da tafarkinsu har zuwa ranar tsaiwa.

Idan ba'a manta ba, muna ci gaba da haskowa wasu abubuwa daga rayuwar magabatanmu ne musamman abinda ya shafi bangaren yanayin ibadarsu, da kuma yadda zukatansu suke narkewa cikin tsoron Allah da kuma tunanin lahirarsu.

Daga cikinsu akwai Ibnu Wahbin watarana ya shiga bandaki sai yaji wani (daga waje) yana karanta ayar nan ta cikin Suratul Ghafir (Wa iz yatahaajjuuna Finnari).

Acikin ayar Allah yana bayanin yadda 'yan wuta suke jayayya atsakanin junansu ne... 

Shi kuwa daga jin wannan Qira'ar nan take ya Fa'di Qasa ya suma.. Har sai da aka wankeshi da ruwan sanyi bai farfado ba.

Ita kuwa Mu'azatul Adawiyyah ('yar uwar Rabi'atul Adawiyyah) ranar da aka kaita dakin Mijinta mai suna Silah bn Ushaym (rah) wani abun Mamaki ne ya faru. 

Shi Mijin ya shiga bandaki, bayan ya fito sai wani 'Dan baffansa ya rakashi wajen amaryarsa, ya shiga yaga daki gyararre da Qamshi da kayan ado..

Bayan fitan 'dan rakiyar, sai Angon ya tashi ya fara sallah (Qiyamullaili) har zuwa Assalatu. Ita ma amaryar haka. Har sai da sukayi kwana da kwanaki ahakan.

Rannan da 'dan baffan nasa ya tambayeshi akan dalilin yin hakan wato mai yasa bai kula amaryarsa ba?. 

Sai yace "Wallahi shigar da nayi cikin bandaki sai ya tunasar dani gidan Wuta da azabarta da warinta.. Sannan kuma shigar da nayi dakin amaryata sai yasa na tuna da gidan Aljannah da ni'imominta. Ban gushe cikin tunani ba. Don haka na tashi tsaye wajen neman gujewa Wuta, da kuma neman Aljannah. (Na manta da zancen amaryar).

Abbas ibnul Waleed ya ruwaito daga babansa cewa Imamul Awza'ee ya kasance idan yana bada karatu duk lokacin da karatu yazo kan ambaton wuta da siffofinta, ba ya dena magana akanta har sai duk wanda ke wajen zuciyarsa ta tsinke!!.

Daga cikin Magabata na kwarai akwai wadanda da zarar sun kalli wannan wutar  ta duniya sai ta tuno musu waccan ta lahirar, har sai zukatansu sun tsorata!

Abu Hayyan Attaymiy yace "Na samu labari tun sama da shekaru talatin cewa watarana Abdullahi bn Mas'ud (ra) yazo wucewa ta kusa da makera suna hura watarsu ta Qira, da ya kalli wajen nan take ta fadi ya suma!.

Imamu Ahmad bn Hanbal ne ya ruwaito. 

Amma Ibnu Abid Dunya ya ruwaito ta hanyar Sa'ad bn Al-Akhram yana cewa "Watarana muna tafiya tare da Abdullahi bn Mas'ud sai muka zo ta kusa da Maqera, sun fito da Qarfe yayi ja-wur awuta suna dukansa. Sai Abdullahi bn Mas'ud din ya tsaya yana kallon abinda sukeyi yana zabga kuka!!".

Domin hakika haka Mala'iku zasu dawwama suna yiwa 'yan wuta.. Wutar tana cin jikinsu, kuma Mala'iku suna bugunsu. Haka zasu dawwama. Babu rayuwa kuma babu mutuwa.

Haka shima Uwaysul Qaraniy (wannan Tabi'in nan mai yawan ibadah) ya kasance yakan ziyarci wajen Maqera yana jin irin gunjin Qarar da wuta takeyi yayin da suke hurata, da kuma yadda Qarfe yake narkewa saboda zafinta.. Chan sai yayi ihu ya fa'di Qasa sumamme!!! (LA ILAHA ILLAL LAAH!!).

Al-A'amash (ra) yace "Wanda yaga Ar-Rabee'u bn Khaytham ya bani labari cewa watarana ya wuce ta kusa da Maqera da ya tsaya ya kalli murhunsu yaga tsananin zafin dake cikinsa, nan take ya fadi ya suma".

Hammadu bn Salamah shima ya bada labarin cewa "Basheer bn Ka'ab da kuma Maluman Qira'ah na birnin Basrah (a Qasar Iraqi) sun kasance suna fita zuwa wajen Makera domin su tsaya su kalli yadda wuta take gunji, sannan su nemi tsarin Allah daga sharrin wutar lahira!!".

To Jama'a kunji fa yadda magabatan namu suke wajen tsoron azabar Allah. To shin mu ayanzu yaya halayenmu suke dangane da wannan? 

Shin ka ta'ba ware wani lokaci domin yin nazari ko tunani akan nau'o'in azabar da Allah yake yiwa masu sa'ba masa? 

Shin ka ta'ba tsayawa kayi tunani game da kwanciyar Qabari, ni'imominsa da azabobinsa da kuma Dubunnan shekarun da zakayi kana kwance acikin naka Qabarin, ko cikin da'di ko wahala?! 

Wallahi 'yan uwa akwai babban aiki agabanmu. Sai dai yawancinmu bamu tsayawa muyi tunani game dashi. Alhalu kuma al'amarin nan yana kan kowanne mutum guda daga cikinmu. Kowa sai ya dandana mutuwa. Kuma kowa sai ya kwanta cikin Qabarinsa. Kafin kuma ranar hisabi.. 

Babban burin Zauren Fiqhu dangane da kawowa wadannan darussan shine don a gudu tare, atsira tare. Lahira ita ce Matabbata. Duniya kuwa mafarki ce. 

Ya Allah kasa mu cika da imani. Ka kyautata karshenmu. Ka kiyayemu daga aikata abinda zai janyo mana tuhuma daga gareka Ya Rahmanu Ya Raheem. 

An gabatar da wannan karatun ne a Zauren Fiqhu 2 da 4. Tun ranar 14-12-2016.

An hada karatun aranar 17-12-2016. (07064213990) Allah yasa mu dace. Ameeen.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI