KAMBUN IDO (MAITA) DA HANYOYIN MAGANCETA DAGA ALQUR'ANI DA SUNNAH
ZAUREN FIQHU:
KAMBUN IDO (MAITA) DA YADDA AKE MAGANCETA (01)
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
Salati da aminci su tabbata bisa Annabin da aka bama Saba'ul Mathaniy da kuma Alqur'ani mai girma, Shugaban Masu fararen gabbai aranar Alqiyamah. Tare da iyalan gidansa inuwar al'ummah, da Sahabbansa yardaddu.
Mun dade muna magana akan matsalar da ta shafi Massul Jinn (shafar Aljanu), Sihiri, da kuma Al-Ainu (kambun ido) ko Maita. Shi yasa yau na kuduri aniyar zan kawo mana wasu hanyoyi guda biyu ko uku wadanda za'a iya bi domin magance matsalar.
Ita dai matsalar Kambun ido gaske ce ba Qarya ba. Domin Manzon Allah (saww) yayi bayaninta Qarara acikin hadisai da dama. Har ma yace "BAYAN QADDARAR ALLAH MADAUKAKIN SARKI, BABU ABINDA YAFI HALLAKAR DA AL'UMMATA FIYE DA KAMBUN IDO".
Kuma yace "DA ACHE AKWAI ABINDA KE RIGA QADDARA AFKAWA KAN MUTUM, TO DA KAMBUN IDO YA RIGATA".
Mafiya yawan masu Kambun ido, basu san ma suna dashi ba. Wadanda kuma suka san cewa suna da abun, basu cika bin hanyoyin da zasu kiyaye kansu daga chutar da al'ummah ba. Sai dai ma su rika amfani da ita amatsayin wani Makami wanda zasu rika yin 'barna dashi acikin mutane.
Kambun ido idan ya afka ma mutum, ko guba (Poison) bai fi shi saurin kisa ko lalata sha'anin mutum ba. Shi yasa da yawa zaka ga mutane suna ta neman maganin karya sihiri, alhali basu san cewa kambun ido ne ya afka musu ba.
Mai kambun ido zai iya yi maka akan dukiyarka ko gidanka ko 'ya'yanka ko lafiyar jikinka, ko aikinka ko kasuwancinka, ko muryarka, ko salon rubutunka, ko yanayin tafiyarka, ko kuma duk wani abu naka wanda ya burgeshi, ko kuma ya jefa hassada acikin baqar zuciyarsa.
Kuma masu irin wannan baiwar (ko chutar) suna nan da yawa acikin al'ummah. Watakil Akwaisu agidanku ko wajen aikinka, ko acikin abokanka ko Ajin da kake karatu, etc.
Sannan kuma akwaisu acikin Aljanu ma, wadanda ta hanyar kallo suke iya chutar da mutum koda basu shiga jikinsa ba.
Kafin inyi bayanin magani, zan fara yin bayanin riga-kafi. Kamar yadda yazo acikin hadisai ingantattu daga Shugaba (saww).
BOYEWA : Akwai bukatar wasu lokutan mutum ya rika boye abubuwan da bayyanasu bai zama wajibi gareshi ba. Ko kuma ma boyesu din zai fi alkhairi.
Misali kamar bayyanar da ado (ga Mace). Dama a shari'ar Allah bai halatta ki rika bayyanar da adonki ga kowa da kowa ba. Sai dai Mijinki, ko kuma 'yan kadan daga Muharramanki wadanda Allah ya lissafa acikin suratun Nur.
Anan nake jan hankalin Matan aure da Bazawarai da 'Yan matan dake sanya hotunansu a Facebook cewa bayan haramcin dake cikin yin haka, kuma lallai suna cikin hatsarin kamuwa da kambun ido.
2. Ba kowacce ni'imah zaka rika bayyanar ma jama'a ba. Kuma ba kowanne mutum zaka rika zantarwa akan abinda ya shafeka ba. Tunda Manzon Allah (saww) yace :
"KU TAIMAKA MA BUKATU DA BOYEWA, DOMIN DUK WANI MA'ABOCIN NI'IMA ABIN YIWA HASSADA NE".
Koda kyakkyawan mafarki kayi, Ance ba kowa zaka rika gaya ma ba, ballantana wani albishir akan harkar kasuwarka, ko aikinka, ko aikinki ko na mijinki.
Hakanan idan wata mota ce dakai ko riga mai tsada ajikinka ko ajikin 'Ya'yanka, bai kamata ka fito kana alfahari dashi a bainar jama'a ba. Domin irin wannan zai iya janyo maka kowacce irin hassada da kambun ido da mugun baki daga wajen mutanen da baka sansu ba ma.
3. ADDU'A : Yana daga cikin manyan hanyoyin Riga-kafi, mutum ya yawaita addu'o'i da zikirorin safe da yamma, Musamman addu'ar neman kariyar Allah daga kowanne sharri.
Misali kamar :
- QUL HUWALLAHU, FALAQI DA NASI (Uku uku safe da yamma, sai kuma Qafa daya bayan kowacce sallah).
"A'UDHU BI KALIMATIL LAAHIT TAMMATI MIN SHARRI MA KHALAQ" (Kafa uku safe da yamma).
"BISMILLAHIL LADHEE LA YADHURRU MA'A ISMIHI SHAY'UN FIL ARDHI WALA FIS SAMA'I WA HUWAS SAMEE'UL 'ALEEM". (Kafa uku safe da yamma).
Sai kuma addu'o'in fita daga gida "BISMILLAH TAWAKKALTU ALAL LAHI. WALA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAH". (Kafa daya yayin da za'a fita daga gida).
Sai kuma addu'ar neman kariya daga sharrin shaitanu da baqin ciki, da kuma masu miyagun idanu :
"A'UDHU BI KALIMATIL LAAHIT TAMMAH MIN KULLI SHAITANIN WA HAMMAH, WA MIN KULLI 'AININ LAAMMAH (Kafa uku safe da yamma).
Sai kuma addu'ar da za'a rika yiwa Qananan yara kafin afita dasu zuwa unguwa ko zuwa wani gidan ko kafin afita wajen biki ko makaranta :
"U'EEDHUKA (IDAN MACE CE SAI ACHE "U'EEDHUKI, IDAN KUMA SU BIYU NE U'EEDHUKUMA) BI KALIMATIL LAAHIT TAMMAH MIN KULLI SHAITANIN WA HAMMAH, WA MIN KULLI 'AININ LAAMMAH" (Kafa uku).
In sha Allahu idan akayi riko da wadannan addu'o'in za'a samu kariya daga sharrin duk wani abin halitta. Ko Shaytanun Aljanu da mutane, ko masu kambun ido.
Anan zamu tsaya, sai a karatu na gaba zamu dora daga inda muka tsaya. In sha Allah.
An gabatar da karatun ne a Zauren Fiqhu Whatsapp - ranar 25-05-2017.
Don Qarin bayani za'a iya tuntubar Zauren Fiqhu ta lambar waya 07064213990 , ko email zaurenfiqhu@gmail.com ko kuma ta hanyar ziyartar babban shafinmu
Comments
Post a Comment