SOYAYYAR MANZON ALLAH (SAWW)
SOYAYYAR MANZON ALLAH (SAWW). ************************************* SON ANNABI (saww) wani hali ne ko dabi'a wanda babu irinsa duk acikin halayen da 'Dan Adam zai iya siffantuwa dasu. Zuciyar da aka tarbiyyantar da ita bisa son Annabi (saww) takan Mance da duk wani abinda ba SHI ba. Kuma bata iya yin wani abu sai cikin koyi dashi. Zuciyar da ta riga ta gaurayu da SON ANNABI (saww) ta kan kasance batta ji, batta gani sai da SHI. Kuma bata yin kowacce Mu'amalar da zata nisantar da ita daga gareshi. Har ta kan kai matsayin yadda ba zata rayu ba, sai da Tunaninsa (sallallahu alaihi wa alihi wa sallam). MISALI : daga cikin Sahabbai akwai THAWBAAN (rta) wanda ya kasance ba ya iya jin dadi arayuwarsa, har sai yazo ya kalli Manzon Allah (saww). Tsawon dare (Awa 12) yayi yawa agareshi. Ba zai iya daurewa har gari ya waye bai ga Annabi ba (saww). Thawbaanu yakan kasa yin barci cikin dare, har sai yazo ya kalli gidan da Manzon Allah (saww) yake ciki. * Sayyiduna KHALID BN WAL