BABBAN TASHIN HANKALI

BABBAN TASHIN HANKALI!!!
*****************************
Hadisi ne zan karanta muku daga Zauren Fiqhu Amma ina neman alfarma guda 'daya awajenku kafin ku karanta hadisin nan... Alfarmar da nake nema awajenku ita ce, ku tsayar da duk abinda kukeyi, ku nutsu ku karantashi da kyau.

Domin na tabbata sai ya girgiza zuciyar duk wani mai Imani

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

Tsira da aminci su tabbata bisa Annabin Qarshe, da dukkan Iyalansa da Sahabbai baki daya.

Yazeedur Raqqaashiy ya karbo hadisin daga Anas bn Malik (ra) yana cewa:

Watarana Mala'ika Jibreelu (as) yazo wajen Manzon Allah (saww) awani lokacin da bai saba zuwa masa ba. Yazo, gaba dayan launin fuskarsa ya chanza. Sai Manzon Allah (saww) yace masa "MAI YASA NAGA LAUNIN FUSKARKA DUK YA CHANJA HAKA?".

Yace "Ya Muhammadu (saww) nazo maka ne awannan lokacin da Allah yayi Umurni da Masu hura wuta suci gaba da Hura ta.

Duk wanda yasan cewa Jahannama gaskiya ce, Wuta gaskiya ce, Azabar Qabari gaskiya ce, kuma Azabar Allah ita ce mafi girma, to bai kamata yayi wani farin ciki ba har sai ya tabbatar da cewa ya samu tsira daga wannan".

Sai Manzon Allah (saww) yace masa "YA JUBREELU INA SO KA SIFFANTA MUN YADDA JAHANNAMA TAKE".

Sai yace "Na'am. Hakika Allah madaukakin Sarki yayin da ya halicci Jahannama, yasa an hurata tsawon Shekaru DUBU. Har sai da ta zama JA - JAWUR. Sannan aka sake hurata tsawon Shekaru DUBU har sai da ta zama FARI - FAT!!

Sannan aka sake hurata tsawon shekaru DUBU har sai da ta zama BAQA - QIRIN!!!.

Tana nan har yanzu BAQA QIRIN ce, mai tsananin duhu ce. Harshen Balbalinta basu mutuwa ballantana Garwashinta.

Na rantse da Girman Ubangijin da ya aikoka da gaskiya, da ache za'a bude misalin kofar allura daga wutar Jahannama, Wallahi sai dukkan Ma'abotan doron duniyar nan sun Qone baki dayansu saboda tsananin zafinta.

Na rantse da girman Ubangijin da ya aikoka da gaskiya, da ache za'a ratayo tufafi guda daya tufafin 'Yan Wutar Jahannama a makaloshi atsakanin Sararin Samaniya, da sai Dukkan Ma'abotan doron Qasa sun Mutu baki dayansu saboda tsananin Warin wannan Tufafin. 😭

Da kuma zafin dake tattare dashi. Babu wanda zai yi saura acikinsu don tsananib abinda zasu riska na zafin wannan tufafin.

Na rantse da girman Ubangijin da ya aikoka da gaskiya amatsayin Annabi, da ache za'a dauko zira'i guda na Sasarin nan na 'yan wuta (wato CHAINS din da ake daure su dashi sannan arika jansu ajan fuskarsu). Wannan Wanda Allah ya ambata Acikin Alqur'ani, a dorashi bisa wani dutse daga duwatsun duniyar nan, da sai dutsen ya narke ya zagwanye har zuwa Qasa ta bakwai.

Na rantse da girman Ubangijin da ya aikoka da gaskiya amatsayin Annabi, da ache za'a ajiye wani mutum a mafa'dar rana ana yi masa azaba, da sai wanda yake mahudar rana ma ya Qone Qurmus saboda bala'in zafinta.

Zafinta mai tsanani ne. Zurfinta mai nisa ne. Tufafin cikinta na Qarfe ne. Abin shan cikinta HAMIMU ne (tafasasshen ruwan azaba) da kuma ruwan Gyambo. Mayafan cikinta kuma an yankosu ne daga Wutar".

Tana da Kofofi guda bakwai, Kowacce Qofa tana da wani yankin cikinsu da aka tsaga mata (zasu shiga ta cikinta) daga Mazaje da mataye.

Sai Manzon Allah (saww) yace: "SHIN KOFOFIN NAN IRIN NAMU NE?".

Sai Jibreelu yace: "A'a sai dai ita kofofin abude suke, wata kofar tana Qasan wata. Tsakanin kowacce Kofa da wata kofar, tsawon tafiyar shekara SABA'IN ne.

Kowacce Qofa ta ninka wacce take sama da ita atsananin azaba har ninki SABA'IN.

Za'a rika kora makiyan Allah cikinta. Kuma duk sanda aka koro wasu ('Yan wuta) zuwa wata kofa, Zabaniyawa ne zasu tarbesu da Sarkoki da Sasarai.

Za'a zira musu Sasari (chains) ta cikin bakinsu sai ya fito ta duburarsu. Sannan za'a daure hannunsa na haggu ajikin wuyansa, hannunsa na dama kuma za'a fasa Qirjinsa dashi aturoshi ta cikin zuciyarsa sai ya fito ta bayan kafadarsa. Sannan ahada adaure da wancan Sarkar.

Kowanne Dan Adam za'a hadashi tare da shaitani guda acikin Sarkar Sasarin, Sannan arika Jansa akan fuskarsa (acikin Garwashin wutar da kuma dagwalonta) Mala'iku kuma suna Jibgarsu da Gudumomin Baqin Qarfe.

Duk lokacin da suka nemi fita daga cikinta saboda bakin ciki da wahala, Sai a sake dawowa dasu cikinta.

Sai Annabi (saww) yace ma Jibreelu (ra) "SHIN SU WANENE MAZAUNAN CIKIN WADANNAN QOFOFI?".

Sai Mala'ika Jibreelu yace: "Kaga amma Qofar nan wacce take chan Qarkashin Qas, ita ce mazaunar Munafukai da kuma wadanda suka kafirce daga Mutanen Annabi Eisa (as) (Wadanda aka ce kar su boye abinci amma sukayi taurin kai suka boye). Da kuma Mutanen Fir'auna.

Ita wannan wutar sunanta "HAAWIYAH".

Sai kuma Qofar nan ta biyu, wadanda zasu shiga cikinta sune MUSHRIKAI. Kuma sunanta "AL-JAHEEM".

Qofar ta uku kuwa masu bautar taurari ne zasu shiga ta cikinta. Sune mazaunan cikinta.  (awani wajen ance zasu zauna tare da masu wasa da sallah).

Kuma sunan wannan wutar "SAQAR".

Qofar wuta ta hudu, ta nan ne IBLIS (L. A.) zai shiga cikinta tare da Mabiyansa da kuma Majusawa masu bautar Wuta. Kuma sunanta "LAZAA".

Qofa ta biyar kuwa ta cikinta YAHUDAWA zasu shiga. Kuma sunanta "ALHUTAMAH".

Qofa ta shida kuwa, NASARA ne zasu shiga ta cikinta. kuma sunanta  "SA'EER".

Daga nan kuma sai Mala'ika Jibreelu ya sunkuyar da kansa yayi shuru, ya kasa ci gaba da magana son jin kunyar Manzon Allah (saww).

Sai Manzo (saww) yace masa "SHIN BA ZAKA BANI LABARIN KO SU WAYE MAZAUNAN CIKIN WANNAN QOFAR TA BAKWAI DIN BA?".

Sai Jibreelu yace: "Sune Ma'abotan Manyan Zunubai daga cikin al'ummarka. Idan har suka mutu basu tuba ba" 

Nan take Sai Sayyiduna Rasulullahi (saww) ya fadi YA SUMA!!!!

Sai Mala'ika Jibreelu ya dauki kansa ya dora akan cinyoyinsa har sai da ya farfado sannan yace:

"YA KAI JIBREELU LALLAI MUSIBA-TA TA GIRMA! KUMA BAKIN CIKINA YA TSANANTA!!! YANZU ASHE AKWAI WANDA ZAI SHIGA WUTA DAGA CIKIN AL'UMMATA?".

Sai yace "Eh amma Ma'abotan Manyan zunubai daga cikinsu".

Daga nan Sai Manzon Allah (saww) yasa kuka, Mala'ika Jibreelu ma yana kuka...!!!".

Ibnu Katheer ya kawo wannan hadisin da ruwayoyi daban daban acikin Littafinsa mai suna AN-NIHAYAH FIL FITAN WAL MALAHIM. Acikin babin dake magana akan wuta da azaba cikinta.

Wannan Darasin yazo muku ne daga ZAUREN FIQHU WHATSAPP (3).

Mun gabatar da karatun ne aranar 9-8-2015. Amma an samu wasu Shaitanun mutane sun kwafa, sun chanza masa launi, sun cire wasu Kalmomi, sannan sun Qara wasu abisa son ransu.

Muna fatan masu yin haka zasu ji tsoron Allah su dena.. Cin amanar ilimi ne. Kuma Allah zai tambayeku akansa.

DAGA ZAUREN FIQHU (11-12-2015).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI