SOYAYYAR MANZON ALLAH (SAWW)

SOYAYYAR MANZON ALLAH (SAWW).
*************************************
SON ANNABI (saww) wani hali ne ko dabi'a wanda babu irinsa duk acikin halayen da 'Dan Adam zai iya siffantuwa dasu.

Zuciyar da aka tarbiyyantar da ita bisa son Annabi (saww) takan Mance da duk wani abinda ba SHI ba. Kuma bata iya yin wani abu sai cikin koyi dashi.

Zuciyar da ta riga ta gaurayu da SON ANNABI (saww) ta kan kasance batta ji, batta gani sai da SHI. Kuma bata yin kowacce Mu'amalar da zata nisantar da ita daga gareshi.

Har ta kan kai matsayin yadda ba zata rayu ba, sai da Tunaninsa (sallallahu alaihi wa alihi wa sallam).

MISALI : daga cikin Sahabbai akwai THAWBAAN (rta) wanda ya kasance ba ya iya jin dadi arayuwarsa, har sai yazo ya kalli Manzon Allah (saww).

Tsawon dare (Awa 12) yayi yawa agareshi. Ba zai iya daurewa har gari ya waye bai ga Annabi ba (saww).

Thawbaanu yakan kasa yin barci cikin dare, har sai yazo ya kalli gidan da Manzon Allah (saww) yake ciki.

* Sayyiduna KHALID BN WALEED (ra) ya kasance ba ya iya yin barci har sai yayita ambaton Manzon Allah (saww).

* Sayyiduna ABDULLAHI BN UMAR (ra) ya kasance ba ya iya gudanar da komai hatta tafiyansa, tsayuwansa, zamansa, cin abincinsa, maganarsa, hawan dokinsa, sai yayi irin yadda ya gani daga Manzon Allah (saww).

Ya kasance bayan rasuwar Manzon Allah (saww) yakan zo ya zauna akusa da Qabarin Mai daraja, ya sunkuyar da kansa kamar wanda yake magana da SHI (saww).

Sayyiduna BILAAL AL-HABASHIY (ra) watarana yazo ziyartar Manzon Allah (saww) bayan rasuwarsa... Sai da yazo gaban Qabarin ya sunkuyar da kansa yana kuka..

Da ya hau kan mimbari yayi Kiran sallah kuwa, SUBHANALLAH!!!! Sai duk garin Madeena ya yamutse!!!

Kuka kakeji ko ta ko ina!!! Sahabbai Maza da Mata, kowa sai kuka!!!!

Saboda wannan kiran sallar nasa, ya tuna musu da Rayuwar Manzon Allah (saww).

Ya Allah ka Qara mana SON ANNABI (saww) da iyalan gidansa da Sahabbansa.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (17-09-2017).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI