IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA (12)
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI. Wannan ita ce fitowa ta goma sha biyu acikin darasin Zauren Fiqhu mai qunshe da bayanin tashin Alqiyamah.. Da fatan za'a karanta da nutsuwa.. Dap da kusantowar ranar Tsayawar Qarshe (wato Alqiyamah) za'a yawaita Samun Khusufi da kuma rikice-rikicen sararin samaniya.. Wannan sararin saman da kake ganinsa yanzu fes dashi, to idan lokacin ya kusanto zata kyakkece ta rika zabalbala tamkar narkakkiyar dalma. Daga nan zata zamanto kamar narkakken mai.. Zata gauraye tare da falakai da farin wata da taurarin cikinta, launinta zai chanza sannan a salu'beta tamkar yadda ake sa'bule gashi daga fatar dabba. Amma yawaitar faruwar Kisifewar rana da wata gabannin wannan, za'a yishi ne domin fa'dakar da rafkanannun zukata da kuma farkar dasu daga barcin shagaltuwar da sukayi game da kusantowar Alqiyamah wacce alamominta basu kyale Mumimi ba, balle kuma wanda ya nutse cikin kogin manyan zunubai.. Daga baya sai Allah (Ubangijin girma d