IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA (12)

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI.

Wannan ita ce fitowa ta goma sha biyu acikin darasin Zauren Fiqhu mai qunshe da bayanin tashin Alqiyamah.. Da fatan za'a karanta da nutsuwa..

Dap da kusantowar ranar Tsayawar Qarshe (wato Alqiyamah) za'a yawaita Samun Khusufi da kuma rikice-rikicen sararin samaniya..

Wannan sararin saman da kake ganinsa yanzu fes dashi, to idan lokacin ya kusanto zata kyakkece ta rika zabalbala tamkar narkakkiyar dalma. Daga nan zata zamanto kamar narkakken mai..

Zata gauraye tare da falakai da farin wata da taurarin cikinta, launinta zai chanza sannan a salu'beta tamkar yadda ake sa'bule gashi daga fatar dabba.

Amma yawaitar faruwar Kisifewar rana da wata gabannin wannan, za'a yishi ne domin fa'dakar da rafkanannun zukata da kuma farkar dasu daga barcin shagaltuwar da sukayi game da kusantowar Alqiyamah wacce alamominta basu kyale Mumimi ba, balle kuma wanda ya nutse cikin kogin manyan zunubai..

Daga baya sai Allah (Ubangijin girma da buwaya) ya umurci Mala'ikansa Israfeelu (alaihis salam) yayi busar farko acikin Qaho.. Wani irin Qaho ne wanda saboda girmansa, da za'a zura dukkan abinda ke doron Qasa acikinsa ba zasu cika rabin rabinsa ba..

Da zarar ya busa Qahon nan, Qararsa zata ratsa cikin sasannin duniya.. Sammai da Qassai, Birni da Qauye da karkara da dazuzzuka da duwatsu da kogonni da ruwaye baki daya... Kowa sai yaji wannan Qarar mai firgitarwa

Duk halittar da taji wannan Qarar nan take zata fa'di Matacciya. Tun daga kan Mala'ikun Sammai zuwa kan Halittun Qassai irin su Aljanu da Mutane, da tsuntsaye da dabbobi da Qwari, sai dai wanda Allah ya kebance daga cikin bayinsa.

Allah Madaukakin Sarki ya fada acikin Alqur'ani : "MU MUNE ZAMU GAJE QASA DA WADANDA KE KANTA, KUMA GAREMU AKE KOMAR DASU".

Lallai dukkan halittun sammai da Qassai zasu mace baki daya, Kuma Allah shi ka'dai zai gajeta (dama tasa ce). Zai wanzu Shine na Qarshe kamar yadda ya tabbata dama Shine na farko.

Allah shine na farkon farko kuma shine na Qarshen Qarshe.. Shine na filin fili wanda hujjojin kadaituwarsa basu 'boyuwa ga bayinsa, Kuma shine na 'boyen da 'boyuwarsa ta hana ganoshi..

Allah yayi tambaya : "MULKI AWANNAN RANAR NA WANENE?".. Babu mai bada amsa. Sai dai wanda yayi tambayar ya bama kansa amsa yace "NA ALLAH NE MAKADAICI MAI RINJAYE".

Wannan ranar tana nan tafe babu kokwanto babu tantama... Kuma babu wanda yasan yaushe ne balle ya gaya maka.. Don haka Ya kai 'dan uwa, yi kokari ka gyatta ayyukanka kafin zuwan nan nata..

Ya Allah ka gafarta mana ka kyautata Qarshenmu kasa mu cika da imani, Aameen. Salati da amincin su tabbata ga Shugaban Larabawa da Ajamawa, Jagoran na farko kuma Cikamakin na Qarshe.. Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa Madaukaka da dukkan mabiyansu har zuwa ranar Qarshe.

AN GABATAR DA KARATUN A ZAUREN FIQHU WHATSAPP RANAR 03/07/2018 18/10/1439. (07064213990).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI