TUBAN MATAR AUREN DA TAYI ZINA DA MADIGO

TAMBAYA TA 2546
*******************
Assalamu alaikum

Ina yini ya hidima da iyali

Wai akwai wata yar uwarta da mijinta yayi tafiya tsawon wata bakwai sha'ani na shaidan da son zuciya wata qawarta ta yaudare ta tayi madigo da ita sau daya sannan ta hadata da wasu maza su biyu tayi zina dasu har ta samu ciki da dayan ta zubar tou tun daga lokacin hankalinta yake tashe na nadamar abin Data aikata.

Watace ta Turo min tambaya Tace dan Allah ka amsa musu

Tou wai malam menene hukuncinta wajen Allah zata iya mika kanta a mata haddi ne na shariar musulunci ko yaya ne? amma dai wai tayi matukar nadama iyaka dan wai tama rabu da wannan qawar tata

Allah ba malam ikon ansa musu ya kuma saka da alkhairi.

AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Hakika wannan baiwar Allah ta zalunci kanta kuma taci amanar mijinta. Ta aikata Madigo tare da zina, wadanda duk suna daga cikin manyan kaba'irori a Musulunci.

Manzon Allah (saww) yace "IDAN MACE TAZO MA MACE (WATO SUKAYI MADIGO) TO SU BIYUN MAZINATA NE".

Sannan acikin wani hadisin wanda Imamul Munziriy ya kawo acikin At-Targheeb yace Manzon Allah (saww) yace "ADUK RANAR ALHAMIS ALLAH YANA YIN GAFARA GA BAYINSA WADANDA BASU YIN SHIRKA, AMMA BANDA MATAR DA ZAMANTO MAZINACIYA".

Sannan kuma abangaren su mazajen dake yin zina da matayen aure, Manzon Allah (saww) yace "MISALIN MUTUMIN DAKE HAWA SHIMFIDAR MATAR DA MIJINTA BA YA NAN, KAMAR MISALIN WANDA MACIJI ZAI YAYYAGA NAMANSA NE DAGA CIKIN MACIZAN RANAR ALQIYAMAH".

(Tabaraniy ne ya ruwaito hadisin).

Bayan laifin zina da madigo ga kuma laifin zubda ciki.. Shima babban laifi ne wanda ko shi kadai ya isheta babban bala'i arayuwar duniya da lahira.

To ya zama wajibi gareta ta yawaita tuba tare da nadama bisa abinda ta aikata, ta yaiwata istighfari kuma ta nisanci wadannan mazinatan da kuma miyagun qawaye. Allah mai gafara ne mai jin qai. Yana karbar tuban bayinsa aduk sanda suka tuba zuwa gareshi. Mutukar sunyi irin tuban da yake so.

Ta yawaita ayyukan alkhairi tare da rokon gafarar Ubangiji mutukar tana raye aduniya. Domin bata da tabbacin shin Allah ya karbi tubanta ne ko bai karba ba!!!. Don haka kada ta dauki abun kamar Qaramin abu.

Anan nake jan hankalin 'yan uwa Mata cewa duk matar da tasan acikin Qawayenta akwai mazinata da 'yan madigo cewa ta nisancesu ta dena Qawance dasu. Domin Allah ya kawomu wani irin zamani wanda mutane basu ganin girman kowanne irin sabon Allah mutukar zasu samu biyan bukata.

Sannan Mazajen dake yin tafiye-tafiyen kasuwanci ko Sana'a ko aikin Gwamnati, ya kamata mutum ya rika tafiya tare da iyalinsa domin kiyaye imaninta da mutuncinta. Mataye da dama masu Qarancin tsoron Allah suna afkawa cikin sabon Allah ta, sanadiyyar muguwar sha'awa da kalle-kallen batsa a social media.

Ki gaya mata tunda har Allah ya rufa mata asiri bao kamata ta tona ma kanta ba. Tayi shuru da bakinta taci gaba da tuba tabi shawarin da aka bata. Allah shi kiyayemu.

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU (26/07/2018 13/11/1439).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI