MU SAN ANNABINMU (31)
Da sunan Allah mamallakin dukkan komai, Salati da amincinsa su tabbata bisa Fiyayyen Annabawansa, Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa madaukaka, da masu biye dasu da dukkan Salihan bayi har zuwa ranar sakamako. Sannan shine kashi na talatin da daya acikin darasin tarihin Ma'aiki (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) wanda ke zuwa daga Zauren Fiqhu Whatsapp. Kuma zamu dora ne daga inda muka tsaya. Idan baku manta ba, a darasinmu na 30 mun tsaya ne akarshen bayanin abubuwan da suka faru a yaqin gwalalo. Yanzu kuma zamu shiga cikin bayanin yaqin da akayi da Yahudawan Banu Quraizah wadanda suka hada baki da kafirai don yaqar musulmai. YAQIN BANU QURAIZAH ************************* Yayin da Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya wayi gari sai ya koma cikin garin Madeenah tare da sauran jama'ar musulmai duk suka ajiye kayan yaqinsu (wato makamai). Shi kuwa Sayyiduna Sa'adu bn Mu'az (radhiyallahu anhu) saboda damuwa d