MU SAN ANNABINMU (31)

Da sunan Allah mamallakin dukkan komai, Salati da amincinsa su tabbata bisa Fiyayyen Annabawansa, Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa madaukaka, da masu biye dasu da dukkan Salihan bayi har zuwa ranar sakamako.

Sannan shine kashi na talatin da daya acikin darasin tarihin Ma'aiki (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) wanda ke zuwa daga Zauren Fiqhu Whatsapp. Kuma zamu dora ne daga inda muka tsaya.

Idan baku manta ba, a darasinmu na 30 mun tsaya ne akarshen bayanin abubuwan da suka faru a yaqin gwalalo. Yanzu kuma zamu shiga cikin bayanin   yaqin da akayi da Yahudawan Banu Quraizah wadanda suka hada baki da kafirai don yaqar musulmai.

YAQIN BANU QURAIZAH
*************************
Yayin da Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya wayi gari sai ya koma cikin garin Madeenah tare da sauran jama'ar musulmai duk suka ajiye kayan yaqinsu (wato makamai).

Shi kuwa Sayyiduna Sa'adu bn Mu'az (radhiyallahu anhu) saboda damuwa dashi da Annabi (saww) yayi, sai yasa aka kafa masa rumfa acikin masallacinsa, domin samun damar kula dashi sosai. 

Ana cikin haka ne bayan sallar azahar sai ga Mala'ika Jabra'eel (wato Jibreelu) amincin Allah ya tabbata gareshi - yazo wajen Manzon Allah (saww) bayan yayi gaisuwa sai yace masa "Shin har kun ajiye makamanku ne?".

Sai yace masa "Eh"

Sai yace : "Mu Mala'iku kam bamu sauke damarar yaqinmu ba. Hakika Allah yana umurtarka cewa ka tafi zuwa ga Banu Quraizah, nima chan zan tafi".

Nan take sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agareshi) ya umurci mai yin shela yayi shelar cewa "Duk wanda ya kasance mai ji ne kuma mai biyayya, kada ya sallaci la'asar fache sai ya isa (kauyen) banu Quraizah".

To anan ne Sahabbai sukayi amfani da abinda suka fahimta. Wasu sun tsaya akan hanyar tafiyarsu suka sallaci la'asar din. Wasu kuma basu sallaceta ba har sai da suka isa Banu Quraizah, alhali alokacin nan har dare yayi. Annabi (saww) duk ya ga abinda kowa ya aikata amma bai ce komai ba. Wato kowanne yayi amfani da fahimtarsa kenan.

Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib (ra) shine farkon wanda ya fita zuwa garin, tare da tutarsa ta yaqi, sannan sauran sahabbai suka biyo baya. Su kuwa yahudawan da suka ga haka sai suka shiga garin nasu suka kukkulle Qofofi.

An zagaye garin har tsawon wata guda da kwana ashirin da biyar babu shiga ba fita. Yayin da yahudawan suka sha wuya sosai sai suka aiko zuwa ga Manzon Allah (saww) cewa a turo musu wani sahabi mai suna Abu Lubabah bn Abdil Munzir (Allah ya yarda dashi) wai zasuyi shawara dashi domin samun mafita. Shi mutumin Madeenah ne kuma yana daga cikin Qabilar ausu ne. Ya kasance abokin huldarsu ne tun a zamanin jahiliyyah.

Yayin da yaje garesu sai suka sanya matansu da 'ya'yansu suka zagayeshi suna ta kuka, har dai tausayinsu ya kamashi. Suka shawarceshi ko yana ganin su sauka bisa duk hukuncin da Manzon Allah (saww) zai yanke akansu?. Sai yace musu "Eh".

Ya fa'di haka kuma yayi isharah zuwa ga makogoronsa, wato yana nufin yanka kenan akansu. To amma yana fa'din haka sai kuma nadama ta kamashi ya fahimci cewa lallai ya ha'inci Allah da Manzonsa tunda ya furta abinda ba'a umurceshi ya furta ba. Don haka ya zagaya ya koma garin Madeenah ya daure kansa acikin masallacin Annabi (saww) kuma yace ba zai bar wannan wajen ba, har sai Allah ya karbi tubansa.

Allah ya karbi tubansa kuma Manzon Allah (saww) ne da kansa ya kunceshi. Kuma wannan  ginshikin da Abu Lubabah ya daure kansa ajiki, har yanzun nan yana nan acikin masallacin Madeenah. Ana kiransa "Ustuwanut Taubah".

Anan zamu tsaya sai a darasi na gaba zamu ji yadda karshen lamarin Banu Quraizah ya kasance. Da kuma hukuncin da aka yanke musu bisa warware alkawarin Allah da Manzonsa (saww) da sukayi.

An gabatar da karatun a Zauren Fiqhu Whatsapp ranar talata 01-10-2019 02/02/1441).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI