MU SAN ANNABINMU (30)

Da sunan Allah Sarkin Sarakuna, Salatai marassa yankewa su tabbata bisa Annabi Muhammadu da iyalan gidansa da Sahabbansa tare da aminci gwargwadon girmansa.

Wannan shine kashi na talatin acikin darasin tarihin Shugaban halittu (saww) wanda ke zuwa daga Zauren Fiqhu. Kuma zamu dora daga inda muka tsaya ne acikin bayanin yaqin gwalalo (Gazwatul Ahzab).

Yayin da wannan sahabi (Sa'adu bn Mu'az) ya samu wannan mummunan rauni sai yai addu'a ga kafirai da yahudawan da sukayi yaudara, yace:

"Ya Allah idan har akwai abinda ya saura daga yaqin Quraishawa, to ka wanzar dani (in halarci yaqin) domin babu wasu mutanen da nafi so in yaqesu fiye da wadannan da suka chutar da Annabinka kuma suka Qaryatashi.

To Ya Allah idan kuma ka kawar da yaqi atsakaninmu dasu, to ka sanya (wannan raunin da akayi mun) ya zamto shahada gareni, kuma kada ka kasheni har sai ka faranta mun raina game da yahudawan banu quraizah".

To dama su Banu Quraizah sun kasance abokan huldarsa ne kuma majibintansa tun zamanin jahiliyyah. To yayi fushi dasu ne saboda yaudarar da suka yiwa Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

Yana yin wannan addu'ar sai jinin dake zuba daga jikinsa ya tsaya chak.

Wanda ya harbi Sa'adu din, sunansa Abu Usamah Al Jashmiy.

Ita kuwa Sayyidah Safiyyah bintu Abdil Muttalib ('Yar uwar mahaifin Annabi sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ita da kanta ta kashe wani bayahude alokacin da yazo yana leken matayen musulmai a inda suke boye.

Ana cikin wannan tashin hankalin ne sai Allah ya kawo taimakonsa ta hanyar wani mutum daga Qabilar Ghatfan mai suna Na'eemu bn Mas'ud  Al Ashja'iy. Yazo wajen Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace masa "Ya Rasulallahi nifa na musulunta alhali saurn mutanena basu san da haka ba. Don haka ka umurceni da duk abinda kaso".

Sai Annabi (saww) yace masa "Duk da cewa kai daya ne, kaje ka wofintar dasu daga garemu, mutukar iyawarka. Domin shi yaqi 'dan yaudara ne".

Daga nan sai ya tafi wajen Yahudawan Banu Quraizah yace musu ''Kun san dai ni masoyinku ne ko?".

Suka ce "ai kai ba abun tuhuma bane agaremu".

To daga nan ya fara gaya musu cewar "Kunga kun hada kai da Quraishawa da Banu Ghatfan kun yaqi Annabi (saww) alhali ku fa nan ne garinku, akwai 'ya'yanku da dukiyoyinku anan. Su kuwa Quraishawa da Banu Ghatfan idan sun samu ganima zasu kwasa, idan kuma wanin wannan ce ta faru, zasu gudu garinsu ne su kyaleku daku da Annabi Muhammadu (saww) alhali kuma baku da karfin da zaku iya yaqi dashi.

Don haka kuce ma Quraishawa ba zakuyi yaqi ba, har sai sun baku wasu manyan mutane daga cikinsu amatsayin jingina awajenku".

Daga jin haka sai Yahudawan suka yarda da shawararsa.

Sai ya fita ya tafi wajen Quraishawa, ya samu Abu Sufyan da sauran wadanda ke tare dashi (shi shine sarkinsu sannan bai musulunta ba) yace masa "Hakika kun dai san irin Qaunar dake tsakanina daku, da kuma cewa bana tare da Annabi Muhammadu (saww) to hakika labari ya sameni cewa Yahudawan nan sunyi nadama kuma har sun aika wa Annabi Muhammadu (saww) cewa "Shin zaka yarda damu idan muka damka maka wasu manya daga cikin jama'ar Quraishawa da Ghatfan, ka kashesu da kanka, sannan mu tayaka wajen yaqar sauran da suka rage?". Kuma ya amsa musu akan haka..

Don haka idan banu Quraizah suka nemi ku basu wasu daga manyan mutanen cikinku kada ku yarda ku basu koda mutum guda".

Daga nan sai ya fita ya tafi wajen Banu Ghatfan yace musu "To ku dai mutanena ne, kuma dangina.... (ya gaya musu irin abinda ya gaya wa Quraishawa).

A daren asabar din cikin wannan watan na Shawwal sai Quraishawa suka aiki Ikrimah bn Abi Jahal tare da wasu jama'a daga Quraishawa da Ghatfan cewa suje suce wa yahudawan su shirya su fito gobe domin su hadu su yaqi Annabi (saww).

Su kuwa Banu Quraizah sai suka ce "Ai mu Yahudawa bama yin yaqi ranar asabar. Kuma mu ba zamu tayaku yaqi ba, har sai kin bamu wasy manyan mutane daga cikinku amatsayin jingina. Domin muna tsoron kada ku gudu zuwa garuruwanku ku kyalemu dashi".

Yayin da wadannan 'yan aiken suka isar da sako zuwa ga Qabilun Quraishawa da Ghatfan, sai duk suka ce "Lallai kuwa Na'eemu bn Mas'ud yayi gaskiya. Ashe dama haka Yahuudawan nan suke?".

Su ma Yahudawan yayin da suka ga Quraishawan sunki su basu jinginar da suka tambaya, sai suka ce lallai kuwa abinda Na'eemu bn Mas'ud ya fa'da gaskiya ne.

Don haka nan take sai kan kafiran ya rarrabu, suka rika jin haushin juna. Kuma awannan daren da sauran dararen dake biye dashi sai Allah ya saukar musu da wata irin iska mai sanyi kuma mai tsananin karfi, tana yaye bukkokinsu, tana ture tukwanen da ake girka abincin mayaqan.

Yayin da Manzon Allah (saww) ya samu labarin halin da kafiran suke ciki sai ya aiki wani sahabinsa mai suna Huzaifa bn Al Yaman yaje sansanin kafirai domin samo cikakken labarin yanayin da suke ciki.

Huzaifah (radhiyallahu anhu) yace "Yayin da na isa sansanin na kafirai sai na tarar dasu iska tare da rundunar Allah tana yi musu kaca-kaca. babu wata wutar da zasu kunna fache sai iskar ta kashe masu. Hakanan tantunansu duk iskar ta rushe.

Sai Abu Sufyan ya mike acikinsu ya sanar da cewa Banu Quraizah fa sun watsar dasu kuma ga iska tana Qara wargaza tanadinsu na yaqi. Don haka shi dai tafiya zai yi..

Nan take dai sansanin kafirai kowa ya watse. Quraishawa sun watse, Ghatfan sun tsere, banu Quraizah kuma jikinsu ya mutu sun rasa yadda zasuyi.

Wannan shine karshen yaqin gwalalo. Kuma Allah ya taimaki Annabinsa ta hanyar aiko da wannan iska mai karfi da kuma fitinar da Na'eemu bn Mas'ud ya afkar atsakanin kafiran.

Kuma tun daga wannan yaqin ne Annabi (saww) yace ba za'a sake kawo ma garin Madeenah hari ba, sai dai su  sukai ma wasu, kuma hakan ce ta tabbata.

Anan zamu tsaya in sha Allah sai a karatu na gaba zamu ji yadda akayi da Yahudawan banu Quraizah.

An gabatar da karatun nan ne a ZAUREN FIQHU WHATSAPP ranar laraba 17/01/1441 17/09/2019.

Salatin Allah da amincinsa su tabbata bisa Annabin Rahma da iyalan gidansa da dukkan zuriyarsa da Sahabbansa baki daya.
www.facebook.com/zaurenfiqhu

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (17/01/1441 17/SEPT/2019
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (17/01/1441 17/SEPT/2019.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI