Posts

Showing posts from 2025

KAMBUN IDO (MAITA) DA HANYOYIN MAGANCETA DAGA ALQUR'ANI DA SUNNAH

ZAUREN FIQHU: KAMBUN IDO (MAITA) DA YADDA AKE MAGANCETA (01) BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM. Salati da aminci su tabbata bisa Annabin da aka bama Saba'ul Mathaniy da kuma Alqur'ani mai girma, Shugaban Masu fararen gabbai aranar Alqiyamah. Tare da iyalan gidansa inuwar al'ummah, da Sahabbansa yardaddu. Mun dade muna magana akan matsalar da ta shafi Massul Jinn (shafar Aljanu), Sihiri, da kuma Al-Ainu (kambun ido) ko Maita. Shi yasa yau na kuduri aniyar zan kawo mana wasu hanyoyi guda biyu ko uku wadanda za'a iya bi domin magance matsalar. Ita dai matsalar Kambun ido gaske ce ba Qarya ba. Domin Manzon Allah (saww) yayi bayaninta Qarara acikin hadisai da dama. Har ma yace "BAYAN QADDARAR ALLAH MADAUKAKIN SARKI, BABU ABINDA YAFI HALLAKAR DA AL'UMMATA FIYE DA KAMBUN IDO". Kuma yace "DA ACHE AKWAI ABINDA KE RIGA QADDARA AFKAWA KAN MUTUM, TO DA KAMBUN IDO YA RIGATA". Mafiya yawan masu Kambun ido, basu san ma suna dashi ba. Wadanda kuma suka san cewa suna d...

HUKUNCIN AUREN KISAN WUTA

AMBAYA TA 153 ****************** Assalamu alaikum Minene hukuncin Auren Dibar wuta a Musulunci? Shin hukuncin Yana da bambanci idan Macce ce ta shirya Auren Dibar wutar ba tareda sanin tsohon Mijinta ba? Minene hukuncin idan matar da Mijin suka shirya Auren Dibar wutar? Sannan hukuncin yana da bambanci idan sabon mijin da Aka Aura yana da Masaniya akan Auren Dibar wuta ne za ayi dashi? (daga Barrister Isma'il) AMSA ****** Wa alaikumus salam wa rahmatulLah. Wannan tambayar mun riga mun amsa irinta achan baya. Amma saboda muhimmancin Mas'alar, da kuma yawan faruwarka acikin al'ummah, sai naga cewa ya zama wajibi mu sake amsa wannan dinma. Imamuz-Zahabiy (rah) ya fada acikin shahararren littafinsa mai suna "KITABUL-KABA'IR" akan shafi na 141, Laifi na 53, yana cewa: Hadisi ya inganta daga Sayyiduna Abdullahi bn Mas'ud (ra) yana cewa: "MANZON ALLAH ﷺ YA TSINEWA MAI AUREN KISAN WUTA, DA KUMA WANDA AKAYI AUREN KISAN WUTAN DOMINSA". Imam Tirmidhy (rah) ...